1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihohin jam'iyyar adawa sun janye karar neman a soke zabe

Binta Aliyu Zurmi
March 4, 2023

Rahotanni daga Najeriya na cewar wasu jihohi 6 daga cikin jihohin da suka shigar da kara gaban kotun koli domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya baiwa Bola Ahmed Tinubu nasara sun janye wannan matakin.

https://p.dw.com/p/4OGIq
Bildkombo Nigeria Wahlen | Peter Obi, Bola Tinubu (M), Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Jihohin da suka hada da Sokoto da Adamawa da Bayelsa da Akwa Ibom da Delta da kuma Edo wadanda gwamnoninsu 'yan Jam'iyyar jam'iyyar adawa ne ta PDP wacce ta zo ta biyu a zaben sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da gaza bin dokokin da ta tsara na gudanar da zaben.

A jiya Juma'a ce jihohin suka janye wannan korafi da suka shigar gaban kuliya ba tare da bada dalilai na janyewar ba.

To sai dai ko baya ga wadannan jihohin da suka janye yunkurin kalubalantar sakamakon zaben da ya gabata , jam'iyyun adawa irinsu PDP da Labour sun sha alwashin ci gaba da kalubalantar wannan sakamakon a gaban kuliya.