1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar tattalin arziki a Najeriya

March 16, 2022

A wani abun da ke zaman alamun fadawa cikin rudanin tattalin arziki, Tarayyar Najeriya na kara shiga matsi duk da tashin farashin man fetur a kasuwar man ta duniya.

https://p.dw.com/p/48a0m
Najeriya I Layuka I Karancin Man Fetur I Gidajen Mai I Abuja
Dogayen layukan sayen man fetur a NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

A Tarayyar Najeriyar dai bisa al'ada, lokacin tashin farashin man fetur na zaman lokacin Owamben mahukunta. Ko bayan cika burin kasafin kudin kasa dai, 'yan mulkin kan kare da asusun rarar kudin man fetur din domin amfani a gaba. To sai dai kuma a yanzu tashin farashin danyen mai na neman jefa masu mulkin da ma talakawa cikin tsaka mai wahalar gaske. Mafi yawan jihohin kasar dai, sun kare ne da biyan rabin albashi a yayin kuma da Abujar ta ce tana shirin cin bashin dalar Amika kusan miliyan dubu biyu duk dai a cikin fatan iya samar da man da 'yan kasar ke nema idanu a rufe. Kuma a cikin tsakiyar rikicin dai, na zaman batun tallafi da ya lamushe daukacin gudunmawar harkar man fetur ga tattalin arziki, sannan kuma ke neman ci mata bashi. Ko bayan batun samar da kudin dai, rikicin man daga dukkan alamu ya kai ga babban rikici na hasken wutar lantarki cikin kasar a halin yanzu.

Zanen Barkwanci I Najeriya I Matsaloli
Zanen barkwanci kan matsalolin da Najeriya ke fama da su

Sau biyu a cikin sa'o'i 48 ne dai, daukacin hasken wutar lantarkin kasar ke rushewa sakamakon matsalar fasa bututun man. Abun kuma da a cewar Abubakar Aliyu  da ke zaman ministan samar da hasken wutar lantarki na kasar, ke barazana ga kokarin wadatar da hasken wutar lantarkin. Ya zuwa yanzu dai ita kanta hajar man fetur din da Abujar ke neman ta wadata, na neman gagarar kundila a kasar da ke tangal-tangal. Layukan mai dai sun gaza kai wa ga bacewa, a yayin kuma da farashinsa a kasuwar bayan fage ke dada tashi. Hankali dai yana rabe a tsakanin warware matsalar makamashin da fuskantar zabe a shekara ta siyasa. Abun kuma da a cewar Dakta Hamisu Ya'u da ke zaman masanin tattalin arziki a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ka iya shafar kokarin gyaran kasa. Sannu a hankali dai man fetur din da kasar ke takama da shi domin samun ci-gaba, na neman komawa kafa ta rusa daukacin tattalin arzikin Tarayyar Najeriyar.