1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mutane sun bace a Najeriya

January 24, 2023

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC ta bayyana cewa akwai kimanin mutane dubu 25 da suka bace ba a san inda suke ba, sanadiyyar riciki da matsalolin tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4MeTA
Najeriya | Boko Haram | Gudun Hijira
Dubban mutane ne dai, suka kauracewa gidajensu sakamakon rikicin Boko HaramHoto: Katerrina Vittozzi/Unicef/picture alliance

Rahoton kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross da aka fi sani da ICRC ya nunar da cewa har yanzu kimanin mutane dubu 26 da suka bace, babu labarinsu sanadiyyar tarwatsewa da suka yi bayan hare-haren Boko Haram a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar. Kungiyar ta ICRC ta ce ya zama dole a karfafa matakai na nemo wadannan mutane, domin a hada su da 'yan uwansu kafin ya kai an manta da su baki daya ganin cewa a nata bangaren ta samu nasarori masu tarin yaawa wajen hada wasu iyalai da danginsu.

Najeriya | Yara | Matsaloli | Boko Haram
Yara da dama sun shiga halin tasku a Najeriya, saboda rikicin Boko HaramHoto: Aminu Abubakar/AFP

Wasu daga cikin mutane da 'yan uwansu suka bace, sun bayyana damuwa tare da neman a taimaka wajen ganin sun dawo gida. Masana da masharhanta dai na ganin tials a hada karfi da karfe tsakanin hukumomi da al'umma da kuma kungiyoyin agaji, idan har ana son samun nasarar mayar da mutanen da su ka bace ga iyalansu ganin da yawa daga cikinsu sun girma kuma da wuya wasu a iya gane su kasancewar sun da kananan shekaru suka bata.