1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakon sakamakon zaben Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 26, 2023

Al'ummar Najeriya na dakon sakamakon farko na zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki na tarayya.

https://p.dw.com/p/4O01q
Mahmood Yakubu
Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa INECHoto: Emmanuel Osodi/imago images

Duk da cewa har kawo safiyar wannan rana ta Lahadi an ci gaba da kada kuri'u a wasu sassan kasar sakamakon wasu dalilai, hakan bai hana al'umma dakon sakamakon farko da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC ke shirn fara sanarwa ba. Daga cikin dalilan da suka sanya ci gaba da kada kuri'a a wasu jihohin dai, sun hadar da halartar jami'ai da kuma kayan aiki a makare da rikice-rikice da kuma tangardar na'ura. Koda yake an samu tahe-tashen hankula a wasu sassan kasar, sai dai masu sanya idanu sun bayyana zaben a matsayin wanda kusan aka kammala shi lami-lafiya. Kimanin 'yan kasar miliyan 90 da suka cancanci kada kuri'a ne dai, suka kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya da aka gudanar a Asabar din da ta gabata. A cewar shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu za a fara sanar da sakamakon zaben na ba da jimawa ba, sai dai samun tsaiko wajen saka sakamakon zaben a shafin Internet na hukumar na haifar da damuwa da ma fargabar yin magudi.