1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Gargadin sojojin Najeriya

January 21, 2020

Wasu bayanai da majalisar Tarayyar Turai ta fitar na nuni da cewa ba a samun nasara a yakin da ake yi da ta’addanci a bakin gabar Tafkin Chadi.

https://p.dw.com/p/3Wc3W
Symbolbild Nigeria Armee
Hare-haren Boko Haram kan jami'an tsaro na kara ta'azzaraHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Bayanan dai na kunshe ne cikin wani kudiri da majalisar Tarayyar Turan ta dauka a makon da ya gabata da kuma ke nuni da cewar harkokin tsaro na kara tabarbarewa a Najeriyar. A wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar ta ce irin wannan kudiri karfafa gwiwa ne ga kungiyoyin kamar Boko Haram, kuma za su iya dakile karsashin dakarun Najeriya na yakar 'yan ta'addan. To sai dai al'ummar shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyan sun tabbatar da karuwar tabarbarewar tsaron, inda suka ce kusan kullum sai mayakan na Boko Haram sun kai hare-hare a sassan jihohin Borno da Yobe tare da hallaka Jami'an tsaro da fararen hula. Ana alakanta karuwar matsalolin tsaro da rashin fahimta da ake samu tsakanin gwamnati da jami'an tsaron da ma janyewar Sojojin kasar Chadi daga rundunar hadaka da ke yakar Boko Haram din a gabar Tafkin Chadi.

Sacewa tare da kisan fararen hula

Nigeria Baga | Truck des IS Gruppe (ISWAP)
Boko Haram na zafafa hare-hare a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

A wani labarin kuma, bayanai sun tabbatar da cewa mayakan na Boko Haram sun kashe shugaban kungitar Kiristoci ta Najeriyar CAN reshen karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa Rev. Lawan Andimi bayan da suka kame tare da yin garkuwa da shi tsawon makonni. Tun a ranar uku ga wannan watan na Janairu ne dai kungiyar ta Boko Haram ta sace shi tare da yin garkuwa da shi, daga bisani kuma kungiyar ta nuna shi a wani sakon bidiyo yana rokon hukumomi da kungiyarsu, da su yi duk mai yiwuwa su ceto shi. Wani dan jarida mai mu'amala da kungiyar wanda kuma yake samun sakwnninta Ahmad Salkida shi ne ya wallafa labarin mutuwar Rev. Lawal Andimi kafin daga bisani wasu jami'an kungiyar ta CAN su tabbatar da mutuwa. An dai shiga rudani dangane da samun labarin mutuwar tasa.
 

Rahotannin dai sun nunar cewa hare-haren mayakan na Boko Haram a kwanakin baya-bayan nan  sun halaka Sojoji da fararen hula a jihohin Borno da Yobe, lamarin da ya bude sabon shafi  na barazanar tsaro da yankin ke fuskanta. Ko da yake jami'an tsaron na cewa shure-shure ne mayakan na Boko Haram ke yi, wanda ba zai hana mutuwa ba.