1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An gudanar da sallar Idi cikin lumana

Abdullahi Maidawa Kurgwi
July 20, 2021

A Najeriya sallar Idi ta gudana a wurare da dama cikin kwanciyar hankali da lumana inda musulmi suka yi tururuwa zuwa masallatai

https://p.dw.com/p/3xkH6
Nigeria Eid Festival Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Sallar Idi ta gudana lami lafiya a jihar Filato. Tun da sanyin safiya al’ummar musulmi suka yi tuturwa zuwa masallatan Idi kamar yadda aka saba cikin farin ciki da walwala. Hukumomi dai sun dauki matakai domin kare aukuwar tashin hankali da kuma tabbatar da tsaro da tsare rayuwar al'umma.

Sai dai ba kamar yadda aka saba a baya ba, a bana sallar ta zo a yanyi na fargabar tsaro da kuma rashin kudi a hannun jama'a

A garin Jos dake jihar Filato an sami tsaikon ababen hawa musamman baburan keke NAPEP wadanda gwamnatin jihar ta Filato ta takaita zirga zirgar su a lokacin bukukuwan sallah.

Kokarin samun bayanai  daga hukumomin tsaro da kuma kwamishinan sufurin jihar Filaton dokar ya ci tura.

Duk da kasancewar ana fama da matsalolin rayuwa to amma al’ummar Musulmi sun yi hamdala kasancewar an gudanar da Sallar cikin farin ciki da walwala.