1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murhun girki mai amfani da hasken rana

Mohammad Nasiru Awal
October 11, 2017

A jihar Tahoua da ke Nijar, wani matashi ya kirkiro wasu murafun girke-girke masu amfani da hasken rana a wani matakin kawo irin tashi gudunmuwa ga yaki da hamada a kasar.

https://p.dw.com/p/2lf5G
Burundi Stromversorgung Solaranlage in Bujumbura
Hoto: DW/A. Niragira

Mamane Arzuka da ke aiki a matsayin jami'in kula da gandun daji da muhalli a jihar Tahoua da ke jamhuriyar Nijar, ya kirkiro da wasu murafun girke-girke masu amfani da hasken rana a wani matakin yaki da hamada sakamakon yawan sare itatuwa don girki a Nijar.

Shi dai wannan matashi ya ce ya kirkiro wannan murhu ne bisa koyi da wani da ya kirkiri wani murhu mai amfani da toka. Amma shi da ya tashi yin na shi, sai ya kirkiro mai amfani da hasken rana, kasancewar Nijar kasa ce mai samun hasken rana kusan kowace rana.

Har yanzu mafi akasarin 'yan Nijar suna amfani da icce wajen girke-girkensu. To ko shin jama'a sun san da wannan fasahar?

"Kadan ne daga cikin al'umma suka sani, domin ban tallata fasahar ba tukuna."

Wata Hajiya Aisha na daga cikin mutanen farko da saye murhun mai amfani da hasken rana kuma ta fara amfani da shi.

Ta ce yanzu kam sun samu canji kuma sun yi bankwana da wahalar da suka dade suna sha na dora tsanwa da icce, abin da ke yi wa lafiyarsu illa.