1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mun gaji dibin bashi - Abba Gida-Gida

Ahmed Salisu
May 29, 2023

Sabon gwamnan kano da ya sha rantsuwar kama aiki Abba Kabir Yusuf ya ce gamnatinsa ta gaji dibin bashi daga gwamnatin da ke barin gado ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

https://p.dw.com/p/4Rw1x
Nigeria Neuer Gouverneur von Kano
Hoto: Kyusufabba/Twitter

A jawabinsa bayan shan rantsuwar kama aiki, sabon gwamnan na Kano da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin kusan Naira biliyan 240 da gwamnatin Dr. Ganduje ta ciyo.

Abba ya ce za su gudanar da bincike kan wadannan kudade don sanin abin da aka yi da su. Wannan batu ya haifar da mayar da maratani iri-iri daga al'ummar ta Kano sai dai ya zuwa yanzu ba wani abu daga ji daga bangaren tsohon gwamnan na Kano.

Dr. Ganduje dai ya shafe shekaru 8 yana jan ragamar gwamnatin Kano karkashin tutar jam'iyyar APC kafin daga bisani APC din ta rasa mulki biyo bayan lashe zaben da Abba Gida-Gida na jam'iyyar NNPP ya yi a 'yan watannin da suka gabata.