1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mummunar ambaliyar ta tilasta kwashe dubban mutane a Rasha

Binta Aliyu Zurmi
April 6, 2024

Rahotanni daga kasar Rasha na cewar sama da mutum 4,000 ne aka kwashe daga yankin Orenburg da ke kan iyaka da kasar Khazakhstan bayan fashewar madatsar ruwa ta dam da ta janyo mummunar ambaliya.

https://p.dw.com/p/4eV8w
Russland Orsk Überschwemmungen nach Dammbruch
Hoto: Administration of the city of Orenburg/AP/picture alliance

Mahukuntan yankin da iftila'in ya shafa sun tabbatar da kubutar da matane 4,208 daga cikinsu 1,019 kananan yara ne.

Sanarwar ta kara da cewar sama da gidaje 2,500 ne mamakon ruwan saman da ya janyo fashewar dam din ya shafa.

Ma'aikatan kwana-kwanan na ci gaba da neman wasu mutamne da ake tunanin ambaliyar ta yi gaba da su.

Binciken da aka fara a kan wannan ibtila'in, an gano harda nuna halin ko in kula da ma rashin gyara wata gada da aka gina a shekarar 2014.

Shugaban kasar Khazakhstan Kassym Jomart wanda ambaliyar ya shafi wani yanki na kasar sa ya ce wannan iftila'in shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta a sama da shekaru 80.