1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Miliyoyin yara na neman tallafi

March 2, 2023

Asusun kula da yara na UNICEF ya ce kusan yara miliyan hudu na cikin halin matsi a yankunan da aka yi girgizar kasa a farkon watan Feibrairun da ya gabata a Siriya.

https://p.dw.com/p/4OBOW
Sansanin wadanda girgizar kasa ta ritsa da matsugunnensu
Sansanin wadanda girgizar kasa ta ritsa da matsugunnensuHoto: Bakr Alkasem/AFP/Getty Images

Babbar darektar Asusun Catherine Russell ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar da ta fitar bayan ziyarar da ta kai yankunan da tuni yaki ya daidai sama da shekaru 10.

Iftila'in girgizar kasar da Siriya da Turkiyya suka fuskanta ta yi ajalin kusan mutane rabin miliyan tare kuma da raba wasu miliyoyi da matsugunnensu baya ga lalata gine-gine masu yawa na al'umma da na gwamnati har da makarantu.

A cewar UNICEF an tsugunar da iyalai da dama a makarantun yankin lamarin da ta ce shi ma babban kalubale ne ga yara wajen ci gaba da samun ilimi.