1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yerima Philip ya mutu

Abdul-raheem Hassan
April 9, 2021

Sanarwar Fadar Buckingham tana cikin jimami mutuwar mijin mai martaba Sarauniyar Ingila mai girma Yarima Philip bayan fama da doguwar jinya.

https://p.dw.com/p/3rm17
Großbritanien I The Duke of Edinburgh |  Prinz Philip
Hoto: Alastair Grant/AP Photo/picture alliance

Fadar Sarauniyar Ingila ta tabbatar da mutuwar Yerima Philip mijin Sarauniya Elizabeth ta biyu, Yeriman ya mutu yana sherkaru 99 a duniya bayan fama da jinya tun watan biyu.

A shekarar 1947 ne Yerima ya auri Sarauniya Elizabeth  shekaru biyu bayan da ta zama Sarauniya, yanzu haka adai suna da yaya hudu da jikoki takwas da Sarauniyar. Su ne dai ma'aura mafi dadewa a gadon sarautar Birtaniya a tarihin masarautar.