1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mexico ta jaddada aiki da Amurka kan dakile bakin haure

December 23, 2023

Shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador, ya ce kasar a shirye ta ke wajen dakile kwararrar bakin haure ba bisa ka'ida ba, inda ya jaddada aiki da hukumomin Washington.

https://p.dw.com/p/4aWK9
Hoto: Cheney Orr /REUTERS

Shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador, ya ce kasar a shirye ta ke wajen dakile kwararrar bakin haure ba bisa ka'ida ba, shugaban ya furta hakan ne a daidai lokacin da ake dakon shigar babbar tawagar gwamnatin Amurka kasar.

Wannan na zuwa ne kwana guda da shugaba Lopez Obrador ya tattauna da takwaransa na Amurka Joe Biden, ta wayar tarho kan yadda za a shawo kan kwararar bakin haure Amurka.

Ya kara da cewa Mexico  za ta sake tsaurara matakan tsaro akan iyakarta da Guatemala, inda ya jaddada bukatar aiki kafada da kafada da hukumomin Washigton.

Rahotanni sun bayyana cewa daga watan Oktoban 2022 zuwa watan Satumbar 2023, kimanin mutum milyan 2.4  ne su ka yi yunkurin tsallaka iyakar Mexico, da suka sha raraka daga jami'an tsaron Amurka masu kula da iyakokin kasar.