1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure 53 sun mutu a hatsarin mota

Abdul-raheem Hassan
December 10, 2021

Adadin bakin haure da suka mutu a hatsarin mota a Mexico ya karu zuwa 53, hukumomi sun ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutane 54 ne suka jikkata bayan da mota dauke da 'yan gudun hijira 200 ta fadi a kan wata gada.

https://p.dw.com/p/446CY
Mexiko Chiapas | Verkehrsunfall mit Migranten
Hoto: El La Mira/REUTERS

Ma'akkatan agajin gaggawa a Mexico na cigaba da aikin ceto, bayan da mutanen da ke cikin motar suka fado kan matafiya da kafa a karkashin gadar.

Wannan hatsarin dai ya faru ne a daidai lokacin da gwamnatocin Amirka da Mexico ke kokarin shawo kan matsalolin kwarar bakin haure tsakanin iyakokin kasahen biyu.