1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Yuganda ya janyo damuwa

Binta Aliyu Zurmi Alex Gitta/SB/MAB
August 10, 2023

Shugaba Yoweri Museveni na Yudanda ya yi kakausar suka ga matakin da bankin duniya ya dauka na dakatar da bayar da rance biyo bayan dokar ladabtar da 'yan luwadi da madigo da kasar ta dauka.

https://p.dw.com/p/4V02e
Yuganda I Shugaba Yoweri Museveni
Shugaba Yoweri Museveni na YugandaHoto: picture alliance/dpa/Russian Foreign Ministry

Shugaba Yoweri Museveni ya yi tir da matakin Bankin Duniya da ya dakatar da bayar da rance da tallafin kudi ga kasar Yuganda sakamakon dokar haramta neman jinsi. sai dai Museveni ya ce ba gudu ba ja da baya a kan sabuwar dokar. Matakin na bankin duniya na iya haifar da nakasu ga tattalin arzikin kasar, saboda tana kokarin ganin ta rage basusukan da ta ciyo daga cibiyoyin kudi na kasa da kasa. Sai dai gwamnatin ta Yuganda ta yi hannunka mai sanda inda ta ce idan bukatar cin bashin ta taso za ta nemi wata hanyar samun rance.

Yuganda 'yan gwagarmaya na LGBTQ
Masu kare hakkin masu neman jinsi daya a YugandaHoto: Bela Varadi/aal.photo/IMAGO

Masu rajin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa na daga cikin wadanda suka yi kira ga babban bankin duniya da sauran manyan kasashen duniya na su dakatar da bada rance da ma agaji ga kasar har sai an janye dokar. To sai dai kamar yadda shugaban kasar ya fada ba gudu ba ja da baya amma ministan harkokin kasashen ketare Okello Oryem wanda ya yi tir da matakin babban bankin ya ce duk da cewar dokar na nan kuma masu neman jinsin suma suna nan amma har yanzu babu wanda aka kama da wani laifi.

Kasar Yuganda ta yi ta shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sakamkon abin da suka danganta da tsangwamar 'yan luwadi da madigo da take yi. Shugaba Yoweri Museveni sai da ya bayyana irin matsin lambar da ma barazana da ya sha tun bayan bayan samar da dokar a ranar 29 na watan Mayun da ta gabata. Wanna sabuwar dokar ta Yuuganda na daga cikin dokoki masu tsananin tsauri a kan 'yan kungiyar ta LGBT a fadin duniya, wanda yanzu haka duk wani da ka kama da laifukan neman jinsi ka iya fuskantar hukuncin kisa.

Dan majalisar dokokin kasar Karim Masaba da ke zama guda daga cikin mambobin kwamitin kudi ya bayyana cewar Yuganda za ta fuskanci radadain wannan mataki na babban bankin, kasancewar babu wani wuri da za su iya samun bashi mai rahusan kudin ruwa. Kasar Yuganda na samun akalla dala biliyan 115 a duk shekara daga babban banki, yanzu haka dakatar da wannan rance zai shafi ayyuka da dama ciki harda babban shirin kawar da fatara a yankunan kasar Yuiganda sama da 50 da ke gabashin kasar.