1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Turjiya da sabon kawancen kasashen Sahel

Gazali Abdou Tasawa SB
April 11, 2024

A Jamhuriyar Nijar 'yan kasar ne suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wasu bayanai da suka nunar da cewa kasar Chadi na neman shiga kawancen AES wanda ya hada kasashen Jamhuyar Nijar da Mali gami da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/4efSt
Burkina Faso, birnin Wagadugu | Taron kawancen AES
Taron kawancen AESHoto: Fanny Noaro-Kabré/AFP/Getty Images

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da a share daya ka samu bullar wani sabon kawancen mai suna Anti-AES wanda ke da nufin yakar kawancen na AES da kuma mayar da kasashen tafarkin dimokaradiyya da kuma a cikin kungiyar ECOWAS/CEDEAO.

Karin Bayani: Bambancin ra'ayi kan rashin bude wasu iyakokin Nijar

Jamhuriyar Nijar, birnin Yamai | Masu goyon bayan fita daga ECOWAS domin shiga kawancen AES
Masu goyon bayan fita daga ECOWAS domin shiga kawancen AESHoto: Hama Boureima/AFP/Getty Images

Ko da shi ke cewa a hakumance kasar Tchadi da kuma kungiyar ta AES ba su kai ga tabbatar da wannan labari na shirin shigar kasar ta Chadi a kawancen kasashen na AES ba, rangadin da wata tawagar ministocin kasar Chadi ta kai a kwanakin baya-bayan nan a kasashen Jamhuriyar Nijar Mali da Burkina Faso ya sanya manazarta da dama fassara lamarin da yinkurin kasar Chadi na shiga kawancen na AES. Malam Bana Ibrahim dan fafutika da ke goyon bayan mulkin soja a kasahen na AES ya bayyana yadda yake kallon lamarin  da kuma sharuddan da ya kamata Chadi ta cika idan tana son a karbe ta a kawancen na AES, musamman ta sallami dakarun Faransa da ke cikin kasar ta Chadi.

Wasu ‘ya Nijar dai na ganin shigar Chadi a kawancen AES zai taimaka sosai a fannin yaki da ta'addanci ta la'akari da rawar da Chadi ta taka a fannin yaki da Boko Haram a kawacenta da Jamhuriyar Nijar da Najeriya da Kamaru a yankin Tafkin Chadi. To sai dai Malam Mahamadou Ismael dan fafutika na ganin bai kamata kasashen AES su amince da kasar Chadi ba.

Jagororin kawancen AES
Jagororin kawancen AESHoto: Balima Boureima/Anadolu/picture alliance

Zawarcin da kasar Chadi ke yi wa kungiyar ta AES na zuwa ne loakcin da share daya a kasar Mali aka samu bullar wata babbar kungiyar mai suna Anti-AES ta ‘yan siyasa da ‘yan fafutika wacce ke da burin yakar kawancen na AES da mayar da kasashen uku kan turbar dimokaradiyya da kuma a cikin kungiyar ECOWAS/CEDEAO. Kuma yayin da wasu ‘yan Nijar ke kawo goyon baya ga sabuwar kungiyar, wasunsu na adawa da ita.

Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga ko wannan hankoro na kasar Chadi na shiga kungiyar AES zai tabbata ko kuma zai ci tura, da kuma tasirin da sabon kawancen na Anti-AES zai yi wajen hana wa kawancen na AES cimma muradun bayan ballewa daga kungiyar ECOWAS/CEDEAO.