1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar janye sojojin Rasha a Mali

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 23, 2021

Kasashen yamma da dama sun yi tir da jibge sojojin kasar Rasha da ke aiki da kamfanin Wagner mai cike da rudani a Mali, inda suka zargi Moscow da taimakawa kamfanin na Wagner a fakaice.

https://p.dw.com/p/44mvh
Zentralafrikanische Republik Bangui | Wahlkampf Präsident
Akwai dai irin wadannan sojojin na Rasha a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Kasashen da suka hadar da Kanada da Jamus da Faransa da Birtaniya da Holland da sauran kawayensu, sun nunar da cewa jibge sojojin na Rasha a Mali zai iya tunzura matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar da ke yankin yammacin Afirka. Wadannan kasashe dai, sun bayyana takaicinsu kan abin da suka kira da cewa gwamnatin rikon kwaryar soja ta Bamako na karkatar da kudin al'umma da dama can bai wadace su ba, zuwa daukar hayar jami'an tsaro daga kasashen ketare domin su taimaki takwarorinsu na Malin.