1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya ja hankali kan ilimin mata

January 24, 2023

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci 'yan Taliban su dawo wa matan kasar da 'yancinsu na neman ilimi

https://p.dw.com/p/4MeTk
UN-Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Selcuk Acar/AA/picture alliance

Albarkacin ranar Ilmi ta duniya, sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira 'yan Taliban su sauya mummunan matsayin da suka dauka na hana mata da 'yan mata damar samun Ilmin sakandare da Ilmi mai zurfi.

Kungiyar UNESCO ta sadaukar da ranar Ilmin ta duniya ta wannan shekarar ga mata da 'yan mata a Afghanistan.

A kasar Afghanistan galibin mata sun tashi haikan wajen kare hakokinsu ta hanyar zanga-zanga inda a mafi yawancin lokuta 'yan Taliban kan yi musu dirar mikiya.

Malaman Jami'oi maza sun ajiye aiki yayin da dalibai maza kuma suka kaurace wa azuzuwa domin nuna goyon baya ga takwarorinsu mata.