1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Majalisar EU na shirin bai wa Von der Leyen damar zarcewa

Zainab Mohammed Abubakar
January 26, 2024

Kawancen jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya ta CDU a Majalisar Turai na shirin bai wa Ursula von der Leyen damar zarcewa a matsayin shugabar hukumar EU a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/4bjcA
Hoto: Petr Stojanovski/DW

Wani babban jami'in Majalisar Tarayyar Turai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, kawancen jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya za ta zabi Ursula von der Leyen a matsayin shugabar Hukumar Tarayyar Turai, idan har ta na muradin zarcewa a karo na biyu, a yayin taron jam'iyyun a watan Maris.

Von der Leyen 'yar jam'iyyar Christian Democrat ta Jamus, har yanzu ba ta fito fili ta bayyana ko tana son wa'adi na biyu na shugabancin kungiyar EU ba, bayan karewar wa'adinta na yanzu a karshen wannan shekarar.

Daniel Caspary, wanda ke jagorantar 'yan majalisar jam'iyyar ta Christian Democrat ta Jamus a majalisar dokokin Turai ya ce,  yana sa ran jam'iyyar ta masu ra'ayin mazan jiya su sake zabarta ta.