1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaganda ta kori Majalisar Dinkin Duniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 4, 2023

Ofishin Hukumar Kula da Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar da cewa zai fice daga kasar Yuganda a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4Umor
Volker Tuerk | Hukumar Kare Hakkin dan Adam | Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker TuerkHoto: Pierre Albouy/KEYSTONE/picture alliance

Ofishin Hukumar Kula da Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniyar a Yuganda ya ayyana hakan ne, biyo matakin da gwamnatin Kampala ta dauka na kin sabunta yarjejeniyar da ta bai wa Majalisar Dinkin Duniyar damar gudanar da ayyukanta a kasar kusan tsawon shekaru 20. Cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ya tabbara da rufe reshensu na Kampala babban birnin kasar, bayan da tuni aka rufe kananan ofisoshin hukumar a Gulu da Moroto. Shugaban hukumar Volker Turk ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, yana mai takaicin rufe ofishin nasu bayan kusan tsawon shekaru 18 suna aikin ceto da ma kare hakkin dan Adam a Yugandan.