1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madugun adawa Hama Amadou ya koma gida

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2023

Tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou da ke adawa da hambararren shugaba kasa Mohamed Bazoum ya koma Yamai bayan shafe fiye da shekaru biyu yana zaman jinya a kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/4WG8r
Hama Amadou ya ahsfe shrkaru biyu a Faransa yana jinya kafin ya koma gida NIjarHoto: Imago/W. Prange

Danginsa da sauran mukarrabansa sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen sanar da dawowarsa gida Nijar. Dama dai bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli, Hama Amadou ya bayyana aniyarsa ta komawa Nijar, domin bada gudunmawa a babban taron kasa da jagoran mulkin soja Janar Adbourahamane Tiani ya yi alkawarin shiryawa.

Karin bayaniNijar: Madugun adawa daga jam'iyyar Lumana

Shi dai Hama Amadou da ya taba zama kakakin majalisar dokoki ya kasance a tsare a gidan yari a Filingué, bisa zargin haddasa tashe-tashen hankula bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da Mohamed Bazoum ya lashe. Duk da hasashen da aka dade ana yi cewa zai taka rawa a zaben shugaban kasa na 2021, amma Hama Amadou bai samu damar tsayawa takara ba saboda hukuncin daurin shekara daya a gidan yari a shari'ar fataucin jarirai, wanda ya bayyana a matsayin "makirci” da aka kulla da nufin hana shi zawarcin kujerar mulkin kasarsa.

Hama Amadou da ya kafa jam'iyyar Lumana ya taba zama firaministan Nijar sau biyu a Jamhuriyar Nijar, na farko karkashin shugabancin Mahamane Ousmane da kuma karkashin mulkin maridayi Mamadou Tandja.