1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafiya Jari: WHO ta yi gardagadi kan Aspartame

Abdourahamane Hassane
August 11, 2023

Aspartame wani sinadari ne da ke kara dandano na zaki wanda ake yi wa sunan kafi suga. Galibi mutane suna amfani da shi a madadin suga yawanci masu fama da ciwon suga.

https://p.dw.com/p/4V2Ec
Illustration | Geträkedose mit Zuckerwürfeln
Hoto: Franziska Gabbert/dpa/picture alliance

Miliyoyin mutane ke yin amfani da wannan sinadari na Aspartame a duniya kuma yana cikin samfuran abinci sama da dubu 6,000 wasu Amirkawa ne masu bincike suka gano sinadarin a shekara ta 1965. 

Hukmar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi a kan sinadarin na Aspartame  da ta ce yana da illa

Aspartam
Hoto: Zerbor/Shotshop/picture alliance

Yawan amfanin da sinadarin wanda kan iya janyo cutar daji ko kansa sotari yakan fara da saka mutum cikin jinya ta rashin lafiya na wasu sasan jikinsa da kan iya tabuwa. Sautari dai mutane arha da rangwame ke kai su yin amfani da wannan sinadari saboda ganin tsadar suga watakilla sun gwammmace kashe kudin kadan domin biyan bukata. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin kan a yi taka tsan-tsan wajan amfani da sinadarin na Aspartame da ke kara dandano na zaki wanda ake yi wa sunan kafi suga.