1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maza na kokarin yakar fyade a Laberiya

Evelyn Kpadeh FD/LMJ
September 22, 2020

A kasar Laberiya matsalar fyade na kara ta'azzara duk da cewa babban laifi ne da ke da hukuncin shekaru 10 a gidan kaso.

https://p.dw.com/p/3iqej
DR Kongo Vergewaltigungsopfer
Mata da yara na fuskantar matsalar fyade a AfirkaHoto: Imago/ZUMA Press

Wannan matsalar dai ta sanya wasu maza a kasar sun fara gangamin wayar da kan al'umma kan yaki da fyade a garin Duazon da ke kusa da Monrovia babban birnin kasar Laberiyan, inda suke tattaunawa kan yadda za su magance matsalar fyade a yankinsu. Shugabanin yankin da malaman majami'u da kuma masu ruwa da tsaki a yankin, na tattauna yadda za su shawo kan matsalar fyaden da ke neman zama ruwan dare gama duniya.

Karin Bayani: Matan Najeriya na tona asirin masu fyade

Daniel Tentay na daga cikin mahalarta taron: "Na shiga taron ne domin tabbatar da wadannan abubuwan ba su faru a cikin al'ummarmu ba, saboda dukkan abun da ya shafi mace ya shafe ni a fakaice domin ina da yara mata biyu kuma ina matukar son su. Mazan da suke fyade mugaye ne, mai ya sa za su haikewa 'yar shekara hudu ko uku da haihuwa? Ai wannan cikakken hali ne na matsafa."

Projekt von Medica Mondiale in Liberia
Kungiyoyin mata sun jima suna yaki da matsalar fyade a LaberiyaHoto: medica mondiale/Sybille Fezer

Tun da dadewa dai, Laberiya ta yi kaurin suna wajen yawan masu aikata fyade da cin zarafi, sai dai lamarin ya kara yin kamari ne a lokacin dokar kulle domin dakile yaduwar annobar coronavirus, wanda hakan ne ya kara wa al'ummar Duazon kaimin yanke wannan hukunci. 

Karin Bayani:Mata sun yi zanga zanga kan fyade a Najeriya

Wannan tattaunawa dai ba a Duazon kadai ake yin ta ba, a birnin Monrovia ma wani dan jarida Trogen Kaizulu ya jogaranci wata tattaunawa da mazan da ke da kwarewa domin samar da hanyoyin magance matsalar: "Mun gane cewa matsalar fyade ba ta sauya zani ba, ta zama matsalar mata da ake barin su su magance abarsu, amma idan muka kalli abun da idon basira, maza ke haifar musu da wannan matsalar. A dangane da haka mun gano cewa akwai bukatar mu maza mu tashi tsaye domin taimaka wa mata yakin, mu kuma fadawa maza 'yan uwanmu, gaskiya cewa mu ne muke aikata cin zarafin kuma ya kamata mu daina."

Karin Bayani: Tsaurara dokoki fyade a Najeriya

Ita ma a nata bangaren gwamnati na kokarin ganin ta yi yaki da matsalar fyade, wanda hakan ya sanya Shugaba George Weah na kasar ta Laberiya, ya saka dokar ta baci kan fyade, tare da nada mai gabatar da kararrakin fyade na mussaman da samar da rijista domin rubuta sunayen wadanda suka aikata fyade da kuma samar da runduna ta mussaman domin yaki da matsalar.