1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 22.05.2023

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
May 22, 2023

Ko lokaci ya yi da alkadarin kungiyar kwallon kafa ta Jamus wato Bayern Munich na lashe gasar Bundesliga karo 10 a jere? Me za a yi a iya kawo karshen nuna wariya a wasanni?

https://p.dw.com/p/4RfIU
Hoto: Roger Petzsche/Picture Point/IMAGO

Bayan da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sha kashi a gida a hannun Leipzig da ci uku da daya a gumurzun da aka yi na mako na 33 a gasar Bundesliga ta kasar Jamus, a yanzu babu tabbacin Bayern din za ta samu nasarar daukar kofin na Bundesliga a karo na 11 a jere. Jim kada bayan kammal wasan dai, mai horas da kungiyar kwallon kafar ta Bayern Munich Thomas Tuchel ya bayyana wa manema labarai cewa:

"Laifinmu ne baki daya kuma dole mu sha kashi a wannan wasa. Ba mu tabuka wani abun arziki ba, sai dai mun yi abin da muka yi a mintuna 30 na farko. Muna kan gaba, sai dai kawai sai muka daina wasa kwata-kwata, muka kuma daina yin duk abin da ya kamata mu yi."

Wannan rashin nasara ta Bayern Munich dai, ta sake bai wa Borussia Dortmund da ke a matsayi na biyu da tazarar maki guda kacal damar sake daura damara. Hakan kuma ya ba ta damar samun nasara a wasan da ta fafata a gidan Augsburg, inda ta samu nasara da ci uku da nema.

Fußball Bundesliga | Mainz 05 vs. Bayern München | Pressekonferenz Thomas Tuchel
Hoto: Thomas Frey/dpa/picture alliance

Kungiyar Manchester City ta zama zakara a kakar Premier League ta Ingila a bana, bayan da ta caskara Chelsea da ci daya mai ban haushi. A baya dai kungiyar Arsenal ta yi ta dakon kofin na Premier, kafin daga bisani ta zubar da makamanta ta hanyar gaza taka rawar gani a wasanninta na baya-bayan nan. Wanna dai ya sanya Arsenal din ta zama 'yar dakon kofin ga Manchester City.

Kimanin mutane 12 sun gamu da ajalinsu a kasar El Salvador sakamakon turmutsitsi da aka samu a filin wasa, yayin da wasu daruruwa suka jikata. Tuni hukumomin kasar da ke yankin tsakiya Latin Amurka suka bayyana kaddamar da bincike bayan faruwar lamarin a karshen makon da ya gabata. Kimanin mutane 35,000 ne suke filin wasan lokacin karawa tsakanin wasu kungiyoyi biyu na kasar ta El Salvador da aka yi turmutsitsin saboda rikici tsakanin magoya baya, abin da ya tilasta jami'an tsaro amfani da karfi domin kwashe mutanen da suke filin wasan.

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Real Madrid ta Spaniya Vinícius Júnior na ci gaba da samun sakonnin goyon baya da karfin gwiwa daga takwarorinsa 'yan wasa har ma da mahukunta, bayan da aka nuna masa wariyar launin fata a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Valencia. Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain da ke Faransa Kylian Mbappé na daga cikin wadanda suka tura sakon goyon bayan ga Júnior mai shekaru 22 a duniya dan asalin kasar Brazil.

Spanien Fußball | Valencia CF v Real Madrid | Rassismus in LaLiga
Hoto: Alberto Saiz/AP/picture alliance

Tun bayan komawarsa taka leda a Spaniya tsawon shekaru biyar da suka gabata, Júnior ke fuskantar kalaman kyama da wariyar launin fata kasancewarsa bakar fata. 'Yan siyasar kasarsa ta asali wato Brazil har ma da Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva da sauran 'yana wasa da kungiyoyi, suma sun fito fili tare da nuna goyon bayansu ga Vinícius. Nan gaba cikin wannan shekara ne ake sa ran gudanar da shari'ar da ta danganci wariyar launin fata da aka nunawa dan wasan gaba na kungiyar Athletic Bilbao Iñaki Williams wanda wani magoyin bayan kungiyar Espanyol ya yi masa a shekara ta 2020.