1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 13.11.2023

Mouhamadou Awal Balarabe
November 13, 2023

Mamelodi Sundows ta Afirka ta Kudu lashe kofin lig kwallon kafar nahiyar Afrika a gaban Wydad ta Maroko

https://p.dw.com/p/4YlJm
Mamelodi Sundowns, zakarun kwallon kafar Afirka
Mamelodi Sundowns, zakarun kwallon kafar AfirkaHoto: SIPHIWE SIBEKO/REUTERS

Kungiyar Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta shiga cikin kundin tarihi na kasancewa ta farko a nahiyar Afirka da ta lashe lig din kwallon kafa da ake wa lakabi da AFL. Wannan nasarar ta samu ne sakamakon lallasa Wydad Casablanca ta Maroko da ta yi a gida Afirka ta Kudu da ci 2-0 a zagaye na biyu na wasan da suka yi, alhali a zagayen farko Sundows ta dibi kashinta a hannun Wydad da ci 1-2. Wannan dai shi ne kofi na farko cikin shekaru shida da Mamelodi Sundows ta zo ta daya a wata muhimmiyar gasa da Hukumar Kwallon kafa ta Afirka ta shirya tun bayan Super Cup a 2017.

Mamelodi Sundowns da shugaban CAF mai ci yanzu Patrice Motsepe ya kafa za ta samu ladar tsabar kudi miliyan hudu na Amurka, baya ga kasance daya tilo da ta lashe irin wannan zubi na gasar da ta zama zakaran gwajin dafi da ta gama manyan kungiyoyi takwas daga yankuna daban-daban na Afirka. Hasali ma daga badi, gasar African Football League za ta fara hada kungiyoyin 24 ciki har da Mamelodi mai rike da kofin a yanzu.

 Mamelodi Sundowns zakarun kwallon kafar Afirka
Mamelodi Sundowns zakarun kwallon kafar AfirkaHoto: SIPHIWE SIBEKO/REUTERS

Tawagogi uku na Afirka da suka fara gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa a Indonesiya sun share wa nahiyarsu hawaye a wasan farko na rukuni da suka buga. Kasar farko da ta yi nasara ita ce Maroko wacce ta lallasa Panama da ci 2-0. Dama dai rabon Lions de l' Atlas ta shiga gasar ta duniya ta wannan rukuni tun 2013 wato shekaru goma da suka gabata. Saifdine Chlaghmo ne ya zura kwallo ta farko a minti  na 16, yayin da Ayman Ennair ya zura bugun daga kai sai mai tsaron gida da Maroko ta ci gajiya a daidai lokacin da Panama ta mamaye ta bayan da aka dawo hutun rabin lokaci.

A nata bangaren, Mali ta mamaye Uzbekistan da ci 3-0 a bisa kwallaye uku da dan wasanta na gaba Mamadou Doumbia a zira a mintuna 30 da 72 da 75. Tuni ma aka fara kwatanta Doumbia da Erling Haaland saboda shahara da ya yi wajen cin kwallo, saboda haka ne Mali za ta ci gaba da dogara a kansa idan za ta yi wasanta na gaba da  Spain. Ita kuwa Senegal mai rike da kofin Afirka na 'yan kasa da shekaru 17 ta doke Argentina da ci 2-1, godiya ta tabbata ga Amara Diouf da ya ci kwallayen tare da ba wa kungiyar Lions de la Teranga damar darewa a saman teburin rukunin D. Ita Senegal da wannan shi ne karo na biyu da take shiga wannan gasa ta duniya za ta yi wasanta na gaba da Poland a ranar Talata. 

'Yan wasan kasar Mali
'Yan wasan kasar MaliHoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Sai dai Burkina Faso ta yi rashin nasara a hannun Faransa ci 0-3, duk da tafiya hutun rabin lokaci da aka yi ba tare da cin kwallo daga bangarorin biyu ba. Sai dai karayar zucci da matasan Burkina Faso suka yi ta sa takwarorinsu na Faransa suka yi musu sakiyar da babu ruwa a mintuna na 49 da 81 da 87. Don haka Burkina Faso ta zama 'yar baya ga dangi a rukunin E, kuma za ta yi wasanta na gaba da da Amurka a ranar Laraba.

Dan wasan kasar Ghana da ya buga wa Black Star wasanni takwas Raphael Dwamena ya rasa ransa sakamakon matsalar zuciya a ranar Asabar a wani filin wasa da ke Albania, inda yake buga wasa tsakanin kungiyarsa KS Egnatia da Partizana. Dama dai Dwamena mai shekaru 28 da ahihuwa ya dade yana fama da matsalar bugun zuciya da ya rikitar da rayuwarsa ta kwallon kafa. Tun a shekara ta 2014 ne ya zo nahiyar Turai, inda ya buga wasa a RB Salzburg da FC Zurich kwallo, inda ya ci  kwallaye 12 a wasanni 18 a kakar wasannin 2017,  kuma ya taimaka wa Zurich wajen cin kambun zakaran Switzerland. Amma matsalarsa ta lafiya ta sa an soke komawarsa zuwa Brighton a bazarar 2017 tare da tilasta masa daina buga kwallo na wani lokaci. Sannan ma ya taba fita hayyacinsa yana tsakiyar wasa a watan Oktoba 2021 a kasar Danmark. Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana (GFA) ta yi gaggawar mika ta'aziyya ga iyalan dan wasan Dwamena yayin da ma'abota kwallon kafa suka nuna alhini game da mutuwar dan wasan, kamar yadda za ku ji cikin wannan rahoto da wakiliyarmu Jamila Ibrahim Maizango ta aiko mana daaga Accra

Raphael Dwamena | dan wasan kasar Ghana
Raphael Dwamena | dan wasan kasar GhanaHoto: Daniel Marzo/Pacific Press/picture alliance

Yanzu kuma sai mu zo gida Jamus inda aka gudanar da wasannin mako na 11 na babban lig kwallion kafa na Bundesliga, kuma har yanzu Bayer Leverkusen ta Koci Xavi Alonso ce ke ci gaba da murza kambunta inda a ranar Lahadi ta bi Union Berlin har gida kuma ta yi mata dukan fitar arziki ci 4-0. Dan wasan baya dan asalin Côte d' Ivoire ya yi amfani a wannan dama wajen zura kwallonsa ta farko a kakar wasa, lamarin da ya faranta masa rai:

"Na yi matukar farin ciki da cin kwallona na farko, na dade ina jiran wannan dama, amma yau mun zabura yadda ya kamata, muna da kocin da yake kara mana kwarin gwiwa a koda yaushe, ba za mu yi barci ba, za mu ci gaba da kasance cikin shiri."

Yanzu dai Bayer Leverkusen na saman teburi da maki 31, yayin da mai horaswarta Xabi Alonso ya kama kafar Pep Guardiola da ya horas da Bayern Munich na shiga sahun wadanda suka yi wasan Bundesliga 11 ba tare da baras da ko wasa guda ba. Hasali ma dai, Leverkusen ta samu nasara a wasanni 10 tare da yin canjaras daya!

Karawar Bayern München da Heidenheim
Karawar Bayern München da HeidenheimHoto: Imago Images/GEPA pictures/T. Bachun

Ita kuwa Yaya-Babba Bayern Munich ta jijjiga a hannun 'yar auta Heidenheim musamman a zagayen farko kafin ta samu nasara 4-2. Sai da ta kai kocin Bayern  Thomas Tuchel ya yi canjin 'yan wasa uku kafin haka ta cimma ruwa sakamakon tsauri da wasa ya yi. Amma kuma zakakurin dan wasanta na gaba Harry Kane da ya ci kwallaye biyu bayan sayo a kan Euro miliyan 100 ya yi nasarar kafa sabon tarihi na cin 17 a wasanni 11 na Bundesliga, ma'ana fiye da wanda Robert Lewandowski ya ci 16 a wasanni 11 a kakar 2019/2020.

Sai dai  a na shi bangaren Serhou Guirassy da ya murmure daga raunin da ya ji ya taimaka wa Stuttgart wajen lallasa Dortmund da ci 2-1. Ko da shi ke Suttgart na a matsayi na a matsayi na uku da maki 21, amma dan wasan gaba dan asalin Guinea Serhou Guirassya ya zura kwallaye 15 ke nan a wasanni tara.

A sauran wasannin kuwa, Möncgengladbach ta lallasa Wolfsburg da ci 4-0, yayin da RB Leipzig ta doke Freiburg da 3-1. Augsburg da Hoffenheim sun tashi wasansu 1-1, haka su ma Bochum da Köln 0-0, yayin da Werder Bremen da Frankfurt suka tashi 2-2, su ma Darmstadt da Mainz sun tashi ba wanda ya ci wani .

karawar Bayern München da Heidenheim
karawar Bayern München da HeidenheimHoto: Imago Images/Pressefoto Baumann/H. Britsch

A sauran manyan lig na kasashen Turai kuwa, Liverpool ta farfado ta hanyar doke Brentford da ci 3-0, kuma ta dauki matsayi na biyu a teburin Premier League da maki 27, duk da cewa tana kankankan da Arsenal da yawan maki. Godiya ta tabbata ga Mohamed Salah wanda ya ci wa Liverppol kwallaye biyu, kuma  ya samu jimillar kwallaye goma a wasanni 12. Sai dai jagora Manchester City na ci gaba da kasancewa a saman taburi da maki 28 duk da tashi da ta yi ci 4-4 da Chelsea.

A Ligue 1 na Faransa kuwa, daga karshe Olympique Lynonais ta lashe wasanta na farko na kakar wasar bana inda ta doke Rennes da ci 1-0, yayin da PSG ta karbe ragamar gasar da maki 27 sakamakon nasarar da ta samu a Reims (3-0) wanda Kylian Mbappé ya ci . Ita kuwa Nice tana a matsayi na biyu da maki 26.