1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Labarin Wasanni 09.10.2023

Suleiman Babayo AH
October 9, 2023

Wani dan kasar Kenya Kelvin Kiptum ya samu nasarar a gasar gudun fanfalaki da ya gudana cikin saÄo cikin sa'oi biyu da minti 00 da dakika 35.

https://p.dw.com/p/4XINn
USA Chigaco | Marathon - Weltrekord - Gewinner - Kelvin Kiptum
Hoto: KAMIL KRZACZYNSKI/AFP/Getty Images

Kelvin Kiptum ya kafa sabon tarihi na kammala gudun cikin sa'oi biyu da dakikoki 35 inda hakan yake zama nasara ta uku da ya samu a kasar bayan lashe wdaanda aka yi a birnin Valencia a shekarar da ta gabata da watan Afrilu a birnin London. Shi dai Kiptum mai shekaru 23 da haihuwa yana cikin wadanda suka yi fice a kasar Kenya a gudun fanfalaki a duniya.

An fafata gasar lig na Pirimiya da Bundesliga

Fußball Bundesliga Eintracht Frankfurt - 1. FC Heidenheim
Hoto: HMB-Media/IMAGO

A gasar lig na Pirimiya da ke wakana a Ingila, kungiyar Manchester United ta doke Brentford 2 da 1, kana Chelsea ta bi Burnley har gida ta lallasa ta 4 da 1. Kungiyar Arsenal ta doke Manchester City 1 mai ban haushi. Kana West Ham da Newcastle sun tashi 2 da 2.A wasannin La Liga da aka kara a Spain, kungiyar Real Madrid ta yi raga-raga da Osasuna 4 da nema, haka ita ma Atletico Madrid ta Real Sociedad 2 da 1, yayin da Granada da Barcelona suka tashi 2 da 2. Sai Jamus inda a wasannin Bundesliga, kungiyar Bayern Munich ta doke Freiburg 3 da nema, sannan Dortmund ta doke Union Berlin 4 da 2. Ana ta bangaren kungiyar Leverkusen da lallasa FC Kolon 3 da nema, haka ita ma Frankfurt ta samu galaba kan Heidenheim 2 da nema.

Moroko da Spain da Portugal za su dauki nauyin kofin duniya na 2030

Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni InfantinoHoto: picture alliance/dpa/XinHua

A karon farko a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake cika shekaru 100 da farata, nahiyoyi za su yi tarayya wajen daukar bakuncinta, lamarin da ke karawa kasashe masu tasowa karfin guiwar shiga takarar daukar bakuncin gasar da ita ce mafi farin jinni a duniya. Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gana da masu bukata na musamman da ke wasan kwallon-kwando a kan keke inda ya bukaci al'ummar kasar su bayar da goyon baya ga masu bukata ta musamman lokacin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya na masu bukata ta musamman da za a yi a birnin Paris na kasar ta Faransa a shekara mai zuwa ta 2024. Shi dai birnin na Paris zai dauki gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a shekarar da ke tafe.