1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Kuri'ar yankan kauna ga Modi

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, inda ake shirin kada kuri'ar yankan kauna ga gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/4V0U6
Indiya | Narendra Modi | Majalaisar Dokoki | Kuri'ar Yankan Kauna
Firaministan Indiya Narendra Modi a zauren majalisar dokokiHoto: Manish Swarup/AP Photo/picture alliance

Jam'iyyun adawar kasar ne dai suka gabatar da kudurin kada kuri'ar yankan kaunar ga Firaminista Narendra Modi bayan kiraye-kiraye ga gwamnatinsa, a kan zubar da jini a yankin Arewa maso Gabashin jihar Manipur da ke barazanar fuskantar yakin basasa. Sai dai ana zargin firaministan ya yi gum da bakinsa kan rikicin da ya barke a yankin, tun a watan Mayun wannan shekarar. Ana dai ganin kudurin kada kuri'ar ba zai yi wata barazana ga gwamnatin Modi ba, sakamakon gwamnatin hadakarsa na da kujeru 331 a majalisar wakilai.