1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kura ta lafa a Kano

June 10, 2014

Lamura sun fara komawa dai dai a Jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya bayan rikicin da ya biyo bayan nada sabon Sarki Sanusi Lamido Sanusi

https://p.dw.com/p/1CGC9
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images

Ana ci gaba da yi wa sabon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi mubaya'a bayan da gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso tare da taimakon Madakin Kano, ya mika masa tagwayen masu, da takobi da wukar dabo tare da takalmin gashin jimina, da kuma malafa, wadannan kaya dai su ne ake bai wa duk wani sarki da aka tabbatar da nadinsa a tarihin Kano, daga nan ne kuma ake kai shi gidan sarki da ke Nasarawa a nada masa rawani sannan a kai shi fadar sarki da ke cikin birni, anan ne kuma za a sara masa sabuwar kofa da zai shiga shi kadai idan kuma ya shiga sai a gine wannan kofa.

To sai dai kuma ga alama har yanzu akwai sauran rina a kaba domin bayan mika wadannan kaya sabon sarkin Sanusi Lamido Sanusi ya ci gaba da zama ne a gidan gwamnatin jiha, maimakon yin tattaki zuwa fadar sarki domin kammala sauran shirye-shirye na al'ada, hakan kuwa ya biyo bayan 'yan sandan da har yanzu suke girke a kofar fadar sarkin.

Emirs-Palast in Kano
Hoto: Tanja Suttor-Ba

Tuni gwamnonin jihohin Najeriya galibi na jam'iyyar APC suka ci gaba da yi wa sabon sarkin addu'ar fatan sa'a, ciki har da gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha, wanda ke cewar wannan nadi yin Allah ne, domin haka a kwantar da hankali.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Suleiman Babayo