1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Kungiyar IS ta sanar da mutuwar shugabanta

Mouhamadou Awal Balarabe
August 3, 2023

Fito-na-fito da mayakan kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) ya yi sanadin mutuwar shugaban IS Abu Al-Hussein al-Husseini al-Qourachi a kasar Sriiya. Ya kasance shugaban IS na uku da aka kashe cikin watanni 18.

https://p.dw.com/p/4UkqN
IS ta shafe watanni kalilan karkashin jagorancin Abu al-Hussein al-Husseini al-QurashiHoto: CPA Media/picture alliance

Kungiyar masu da'awar jihadi ta IS ta sanar da cewa an kashe shugabanta Abu Al-Hussein al-Husseini al-Qurachi a wata arangama da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) a yankin Arewa maso yammacin Siriya. Kakakin kungiyar IS ne ya yi wannan shelar a wani sauti da aka watsa a manhajar aika sako ta Telegram ba tare da bayyana lokacin da aka kashe shi ba.  Wannan dai ya kasance shugaban IS na uku da aka kashe a cikin watanni 18, yayin da Khalifanta na farko  Abu Bakr al-Baghdadi ya gamu da ajalinsa a Idlib a Oktoban 2019.

Kungiyar da ke gaggwarmaya da makamai ta bayyana Abi Hafsan al-Hashimi al-Qurashi a matsayin shugaba na biyar na IS da aka nada. IS ta fara mamaye yankuna da dama na Iraki da Siriya shekaru taran da suka gabata, kafin ta durkushe sakamakon farmakin taron dangi da aka yi ta kai mata, ko da shi ke tana ci gaba da kai hare-hare a kasashen biyu.​