1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun Masar ta daure jagoran adawa Ahmed al-Tantawi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 7, 2024

Wata kungiyar kare hakkin jama'a EIPR ta ce baya ga hukuncin daurin shekara guda, an ci tarar al-Tantawi Dalar Amurka 647, da haramta masa shiga zabe har na tsawon shekaru 5, bisa laifin karya ka'idojin yakin neman zabe

https://p.dw.com/p/4c8Tj
Hoto: AHMED HASAN/AFP/Getty Images

Wata Kotun kasar Masar ta zartar da hukuncin daurin shekara guda ga 'dan adawar gwamnati Ahmed al-Tantawi, wanda a bara ya so tsayawa takarar shugabancin kasar don fafatawa da shugaba Abdel Fattah al-Sisi.

Karin bayani:Masar ta kama makamai a kayan agaji zuwa Gaza

Wata kungiya mai rajin kare hakkin jama'a ta EIPR ta ce baya ga hukuncin daurin shekara guda a gidan yari, kotun ta ci tarar al-Tantawi Fan din kasar dubu ashirin, daidai da Dalar Amurka 647, tare da haramta masa shiga zabe har na tsawon shekaru 5, bisa samunsa da laifin karya ka'idojin yakin neman zaben shekarar da ta gabata.

karin bayani:Habasha da Masar sun gaza cim ma matsaya kan Kogin Nilu

al-Tantawi dai ya janye shiga zaben watan Disambar bara ne bayan da ya yi zargin muzguna masa da hukumomi suka rinka yi.