1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Volkswagen ya yi choge a motocinsa

May 25, 2020

Wata kotun Jamus ta zartas da hukuncin cewa kamfanin kera motoci na  Volkswagen ya biya mutanen da ke amfani da motocinsa diyya.

https://p.dw.com/p/3cjaj
Logo Volkswagen
Hoto: picture-alliance/dpa/H. C. Dittrich

Kotun ta ce sanya na'urar boye adadin hayakin da motocinsa ke fitarwa, wani babban kuskure ne da kamfanin Volkswagen ya tabka. Kafin hukuncin na wannan Litinin, wata karamar kotu a Jamus ma ta zartas da irin wannan hukunci.

Stephan Seiters alkalin Kotun Tarayya ta Jamus ne ya tabbatar da hukuncin karamar kotun da ya bukaci kamfanin Volkswagen ya biya diyya. 

A shekara ta 2015 wasu kwararru a Amirka suka fara fallasa wannan choge da kamfanin  Volkswagen ya yi wa motocinsa wurin milyan goma sha daya. Tuni kuma bayan sanar da hukuncin na wannan Litinin kamfanin  Volkswagen ya sanar da cewa zai fara tattaunawa da masu irin wadannan motoci.