1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta kama dan bindiga Faransa da laifin kisa

Binta Aliyu Zurmi
December 27, 2022

Kotu a Faransa ta kama dan bindiga da ya hallaka Kurdawa uku da laifin kisa da kuma yunkurin kisa gami da mallakar bindiga ba da izini ba.

https://p.dw.com/p/4LRct
Frankreich Die kurdische Gemeinde demonstriert in Paris
Hoto: Michel Stoupak/NurPhoto/picture alliance

Wata kotu a Faransa ta kama dan bindigar nan na birnin Paris da ya kai hari a cibiyar al'adu ta Kurdawa a birnin Paris a ranar Juma'ar din da ta gabata da laifin kisa.

Mutumin mai shekaru 69 ya amsa laifin nuna tsananin kiyaya ga baki, alkalin ya sameshi da laifin kisa da kuma yunkurin kisa bisa wariyar da kabilanci da kuma addini gami da laifin mallakar bindiga ba tare da izini ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake tuhumar wannan mutumin da nuna wariya ba, lamarin da al'ummar Kurdawar da ke Paris suka ce jami'an tsaro ba su yi abin da ya kamata ba na hana aukuwar wannan harin da a wannan karon ya hallaka mutane.

Harin na wannan lokacin ya fama wani tsohon gyambo da ke zukatan Kurdawa, wanda a shekarar 2013 an kai wani makamacinsa  a kansu.

Daruruwan mutanen ne suka gudanar da gangamin yin tir da nuna wariya a tsakanin al'umma.