1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kosovo ta zama ƙasa mai cikkaken 'yanci

September 10, 2012

Kasashen duniya da dama sun yi marhabin da sabuwar ƙasar Kosovo

https://p.dw.com/p/166Lg
A Kosovo Albanian girl is holding a Kosovo flag as Kosovo Albanians take to the streets to mark the first anniversary of their declaration of independence from Serbia in Pristina, Kosovo on 17 February 2009. Kosovo declared independence on 17 February 2008. Recognised as independent by more than 50 countries including the United States and most EU states, but not recognised by others including Russia, China and Serbia, Kosovo's political stability is precarious. EPA/ERMAL META +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan shekaru huɗu da rabi da ɓallewa daga Sabiya, ƙasar Kosovo ta yi bikin samun cikkaken 'yanci.

A yammacin wannan Litinin a birnin Pristina, babban birnin ƙasar, Komitin ƙasashe 25 da ya jagorancin ɓallewar Kosovo ya aje aiki, domin miƙawa hukumomin ƙasar ragamar al'amura gaba ɗaya.To saidai wannan komiti tare da haɗin gwiwar tawagar ƙungiyar tarayya Turai, zai ci gaba da sa ido har sai lokacin da ƙasar ta zauna da gindinta.

Daga bayana 'yancin kan ƙasar Kosovo a shekara 2008 zuwa yanzu ƙasashe 90 na duniya suka amince da ita.To saidai Sabiya na adawa hakan, amma ƙungiyar tarayya Turai ta gittawa hukumomin Sabiya sharaɗin ƙulla kyakkyawar ma'amala da Kosovo, kamin Sabiya ta samu karɓuwa a matsayin memba a sahun ƙasashen EU.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe