1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirimiya: Putin da Zelenskiy sun tattauna

Ahmed Salisu
July 11, 2019

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya tattauna ta wayar tarho da sabon shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy kan rikicin da ke cigaba da wakana a gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/3LwmF
Karte Ukraine Russland Sewastopol ENG

Tattaunawar wadda ita ce irinta ta farko da Putin din ya yi da takwaransa na Ukraine tun bayan da ya dare kan gadon mulki ta kuma tabo batun sakin fursunonin yaki inda suka amince kan kwararru daga kasashen biyu su tattaunawa don samun cimma matsaya.

Gabannin zantawar da shugabannin biyu suka yi dai, Shugaba Zelenskiy ya nemi yin zama na musamman da shugaban na Rasha a birnin Minsk na kasar Belarus don zantawa kan yankin Kirimiya sannan ya bukaci Rasha da ta saki sojin ruwanta da ta kame bayan wata 'yar hatsani da aka yi cikin watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Tuni dai ofishin shugaban na Rasha ya bayyana cewar a shirye shugaban yake kan su zauna da sabon shugaban na Ukraine sai dai ya ce da wuya a iya yin wannan zama kafin zaben majalisar dokokin Ukraine din wanda zai gudana ranar 21 ga wannan watan da muke ciki.