1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta harba tauraron dan Adam na farko

April 15, 2023

Bayan wasu 'yan lokuta, Kenya ta yi nasarar harba wani tauraro da masana kimiyya suka samar. Daga Amirka ne dai aka harba na'urar da ake ganin za ta taimaka wa kasar.

https://p.dw.com/p/4Q8lZ
Hoto: Paul Hennessy/AA/picture alliance

Kasar Kenya ta kaddamar da taurarun dan Adam na farko wanda kwararrun masana kimiyya 'yan asalin kasar suka kirkiro.

Tauraron na dan Adam wanda kamfanin Space X ya harba daga birnin California na kasar Amurka, an kera shi ne da nufin samun bayanan kimiyya da za su inganta harkokin noma da ma sa ido kan al'amuran da suka shafi muhalli.

Sau da dama ne aka yi ta dage aikin harba tauraron zuwa sararin samaniya cikin wannan makon, saboda rashin kyawun yanayi.

Kasar ta Kenya dai na daga cikin kasashen yankin gabashin Afirka da ke fama da matsaloli na yanayi, musamman na bala'in fari da ke haddasa tsananin karancin abinci da ma ke kare dabbobi.