1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Kawance tsakanin Shugaba Barrow da Yahya Jammeh

September 10, 2021

Al'ummar Gambiya sun kadu da jin cewa Shugaba Adama Barrow ya kulla kawance da tsohon Shugaba Yahya Jammeh, gabanin zaben kasar da zai gudana a watan Disamban bana.

https://p.dw.com/p/40Amv
Tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh (hagu) da shugaba mai ci Adama Barrow (dama)
Tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh (hagu) da shugaba mai ci Adama Barrow (dama)

Babban abin da yaryejeniyar kawancen ta kunsa shi ne, za a bar Yahya Jammeh ya dawo kasar cikin mutunci a matsayinsa na tsohon shugaban kasa, yayin da ita kuwa jam'iyyar APRC ta Jammeh, za ta mara baya wa shugaba Adama Barrow a zaben da ke tafe.

Wasu daga cikin mutanen da suka dandani radadin mulkin Yahya Jammeh sun kwatanta shugaba Adama Barrow na jam'iyyar NPP, a matsayin maciyin amana bisa wannan yarjejeniyar da aka kulla, wasunsu na cewa ko barci ba sa yi tun lokacin da labarin ya zo musu. Jammeh dai kungiyar ECOWAS ta tilasta masa yin hijira zuwa kasar  Equatorial Guinea tun kayen da Adama Barrow ya yi masa. Shugaban riko na jam'iyyar Jammeh, Fabakary Tombong Jatta ya fada wa magoyan jam'iyyar cewa sun kulla kawance da Adama Barrow, kuma wannan tsarin ya samu amincewar Yahya Jammeh, "a wannan yarjejeniyar kawance tsakanin jam'iyyun namu an saka mata hannu ranar biyu ga watan Satumban 2021."

Karin bayani: Gambiya: Adama Barrow ya cika watanni shida a kan mulki

Sai dai wannan labarin bai yi wa mutanen da suka sha azaba a zamanin mulkin Jammeh dadi ba, a cewar shugaban cibiyar kula da hakkin wadanda aka ci zarafinsu Sheriff Kejira.

Kayen da Jammeh ya sha a hannun Adama Barrow a zaben 2016 ya zo da mamaki
Kayen da Jammeh ya sha a hannun Adama Barrow a zaben 2016 ya zo da mamakiHoto: Reuters/T. Gouegnon

"Adama Barrow bisa dukkan alamu maciyin amana ne, shi maci amana ne, kuma shi abin kaito ne ga al'ummar Gambiya. Wannan shi ne cin amana cikin wannan karni da zan iya ambato."

Ensa Njie masanin siyasa da ke jami'ar Gambiya, ya ce kawancen jam'iyyun Barrow da Jammeh wata gagarumar gamayya ce.

"Zai yi wuri mu ce hadakar jam'iyyun biyu tabbas za su yi nasara. Ta yiwu mu sake ganin wani kawance da zai tabbatar da kada jam'iyya mai mulki kamar yadda ta faru a 2016, don haka yanayin zai iya canzawa cikin kwanaki ko a cikin makwanni."

Kawo yanzu dai kashi 73 cikin 100 na 'yan Gambiya bincike ya nuna suna bukatar a tasa keyar Jammeh zuwa gida don hukunta shi. A ra'ayinsu yin wannan shi ne yin adalci ga jama'ar da mulkin Jammeh ya ci zarafinsu. Yayin da su kungiyoyin fafutaka ke cewa ya zama wajibi shugaba Adama Barrow ya aiwatar da rahoton da aka rubuta bayan kafa hukumar sasantawa da yafiya tsakanin 'yan Gambiya bayan mulkin Jammeh.