1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Tallafin koyarwa kyauta

March 29, 2017

Wasu matasa a jihar Katsina da suka kammala karatun gaba da sakandare sun himmatu wajen bada gudummuwa ta fuskar ilmi, inda suke koyar da karin darasi ga yaran unguwanninsu a lokutan hutu.

https://p.dw.com/p/2aEtg
Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Wadannan matasa wadanda ba su da aikin yi sun sadaukar da kansu suna koyarwa a makarantun gwamnati kyauta maimakon su zauna haka nan, kuma hakan na taimakawa wajen bunkasa ilmi ganin ana fuskantar karanci malamai a kusan ko wace makaranta a jihar Katsina.

Matasan da ke garin Jani a Katsina suna bada wannan gudummuwa ne a makarantun firamare da sakandare don habaka ilmin yara da kuma dakile yawace-yawace musamman lokacin hutu. Kamar yadda shugabansu Abdullahi Garba Jani ya bayyana:

"Da kashin kanmu muka zauna muka yi tunani muka ga ya kamata tun da dai muna da yawa, wadanda suka samu dama suka samu wucewa karatun gaba da sakadare. Wasunmu sun yi Diploma wasu NCE wasu kuma ma Digiri, sai muka ga cewa to tunda mun samu wannan damar sai muka ce bari mu tattara kanmu mu rika koyar da su lokacin hutu."

Tansania Schüler Symbolbild
Hoto: picture-alliance/robertharding

Wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin sun kasa boye jin dadinsu:

"Sunana Amina Sani, a gaskiya wannan koyarwa da ake mana zai kara inganta karatunmu don haka za mu kara bada kwazo don samun ilimi mai inganci mun gode."

"Sunana Shafi'u Ibrahim, a gaskiya wannan koyarwa da ake mana zai taimaka mana don cigaban rayuwarmu."

Mai shari'a Sadik Mahuta mai murabus wani mai karfafa wa matasa gwiwa ne a jihar Katsina musamman ta fuskar ilimi, wanda ya jinjina wa matasan kuma ya sha alwashin bada gudummuwa garesu don ganin an dakile matsalar da ilimi ke fuskanta a jihar ta Katsina.