1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen siyasar Ganduje da El-Rufa'i

Nasir Salisu Zango IY/LMJ
April 17, 2024

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na Kano da takwaransa na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i na fuskantar kalubalen siyasa.

https://p.dw.com/p/4etZI
Najeriya | Kaduna | Majalisa | Bincike | Tsohon Gwamna | Mallam Nasiru El-Rufai
Tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2023 ne, Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi gwamnan KadunaHoto: picture alliance/AA/Stringer

Rikicin siysar na jihar Kano dai, na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Kaduna a Najeriyar, ta kafa kwamitin binciken dukkanin basussukan da tsohon gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya ciwo da kwangiloli da ma bankado harkallar da ake zargin gwamnatin ta tafka tare da sauran ayyukan da aka dakatar. A wani zaman gaggawa da majalisar dokokin Kadunan ta gudanar kan bukatar binciken tsohun gwamnan kaduna da sauran makarrabansa an bai wa kwamitin binciken bin bahasin wa'adin wata guda, domin tattara rahoton da za a gabatar a gaban 'yan jarida. Kwamitin dai, zai gayyaci duk wani jigo a gwamnatin El-Rufai da suka hada da kwamishinoninsa da tsohon kakakin majalisa da hadimansa na kusa da kuma shugabannin ma'aikatun gwamnatin da suka yi aiki a lokacinsa. Al'ummar jihar ta Kaduna, na fatan ganin an yi adalci wajen gabatar da rahoton.

Najeriya | APC | Shugaba | Jam'iyya | Abdullahi Umar Ganduje | Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

Binciken na El-rufa'i dai na zuwa ne a daidai lokacin da asana da sauran al'umma a jihar Kano, ke ci gaba da fashin baki da martani kan umurnin babbar kotun jihar dangane koken da wasu kusoshin jamiyyar APC a mazabar Ganduje suka kai gaban kuliya da ke neman tabbatar da dakatar da Gandujen daga jam'iyyar ta APC. Wasu dai na ganin matakin kotun karkashin Mai Shari'a Usman Na'abba na bayar da takaitaccen umurnin cewa a tsaya a matsayar da ake kai a ranar 15 ga wannan wata na Afirilu da muke ciki, ya tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC me mulki a kasar Dakta Abdullahi Umar Gandujen. A ranar ta 15 ga watan na Afirilu da muke ciki, aka ayyana dakatar da Gandujen. Sai dai wani abu da ya mayar da umurnin ya zama mai harshen damo shi ne, a wannan ranar ce dai wasu kusoshin jam'iyyar ta APC a mazabar Gandujen da kuma karamar hulumar Dawakin Tofa sun yi watsi da dakatarwar.