1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kamfanin Shell zai biya manoman Najeriya diyya

January 29, 2021

Bayan kwashe shekaru 13 ana tafka shari'a, a karshe kotun kasar Holland ta tilasta wa kamfanin mai na Shell da ya biya wasu manoman kudancin Najeriya diyya.

https://p.dw.com/p/3oZrr
Nigeria Ölverschmutzung Öl Ogoniland
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb/M. A. Johnson

Wata kotun daukaka kara ta kasar Holland ta umurci kamfanin mai na Shell da ya biya diyya ga wasu manoma a yankin Naija Delta da ke kudancin Najeriya, bayan samun kamfanin da laifin gurbata filayensu na noma.

Wata kungiyar fafutikar kare muhalli mai suna Friends of the Earth, ita ce ta taimaka wa manoman na Naija Delta wajen kalubalantar kamfanin a shekara ta 2008.

Kotun ta ce kamfanin na Shell ya biya diyyar ga wasu manoma hudu da suka shigar da karar.

Tuni kuwa kungiyar ta Friends of the Earth, ta yi marhabin da da wannan hukuncin da kotun ta yanke a yau Juma'a, tana mai cewa hakan nasara ce gagaruma ga kokarin kare muhalli da ma mutanen da ke rayuwa a kananan kasashe na duniya.