1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran 'yan awaren kasar Kamaru zai daukaka kara

Zulaiha Abubakar
September 3, 2019

Rahotanni daga Yaounde babban birnin kasar Kamaru san bayyana yadda jagoran 'yan aware Julius Ayuk Tabe tare da magoya bayansa zasu nemi daukaka kara a hukuncin daurin rai da rai da kotun sojoji ta yanke musu.

https://p.dw.com/p/3OxlL
Präsidentschaftswahl in Kamerun Sicherheitskräfte
Hoto: DW/F. Muvunyi

An gurfanar da Ayuk Tabe a gaban kuliya bisa samunsa da laifuffukan balle wani yanki daga kasar ta Kamaru da kuma ayyukan ta'addanci kafin yanke masa hukuncin mai tsauri a watan da ya gabata, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai Joseph Fru shugaba a ayarin  lauyoyin da ke kare 'yan awaren ya bayyana cewar kotun ta yi gaggawar yanke hukunci ba tare da baiwa wadanda ake zargin damar kare kansu yadda ya kamata ba, duk kuwa da cewar sai da kotun ta gabatar da gamsassun shaidu. Kari kan hukuncin da aka yankewa jagoran adawar da mataimakansa akwai tarar kudaden da yawansu ya kai Euro miliya 400 saboda asarar dukiyar da suka haifar a kasar.

Ayuk Tabe mai shekaru 54 kuma kwararre a fannin kimiya da fasahar na'ura mai kwakwalwa, ya kasance mutum na farko a tarihin Kamaru da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Ambazoniya.