1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kyamar Faransa na janyo juyin mulki a Afirka

Isaac Kaledzi LMJ
August 16, 2023

Kwararru na danganta matsalar da karuwar talauci da kuma karancin kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labarai da ke da tasiri da kuma gagarumin tasirin da Faransan ke da shi a kasashen da ta yi wa mulkin mallakar.

https://p.dw.com/p/4VF6R
Jamhuriyar Nijar | sojoji | Kyama | Faransa
Zanga-zangar kyamar Faransa a Jamhuriyar NijarHoto: AFP/Getty Images

Tun a shekara ta 2020, aka fara fuskantar rikicin siyasa a kasashen yankin Afirka ta Yamma rainon Faransa. Da dama dai na ganin yadda Faransa ke ci gaba da daukar kasashen Afirka da ta yi wa mulkin mallaka a matsayin wani bangare nata, na da nasaba da wadannan matsaloli. Wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam a Senegal da ke tare da gidauniyar Open Society Ibrahima Kane ya shaida wa DW cewa, bukatun ballewa daga tasirin Faransa gaskiya ne. Ya kara da cewa: "Gaskiyar cewa Faransa ba ta sauya tunaninta a kan Afirka da 'yan Afirka ba, ita ce ta yi mana mulkin mallaka. Koyaushe Faransa ba ta daukarmu da wani muhimmanci. Tana daukar al'ummar Afirka musamman wadanda ta yi wa mulkin mallaka a wani abu dabam. Al'ummar Afirka ta Yamma musamman rainon Faransa, suna son abubuwa su sauya a daina kallonsu a matsayin 'yan Afirkan Faransa a gansu a matsayinsu na 'yan Afirka. Al'ummar da ke da cikakken 'yanci a duniya da nasu tunanin na kashin kai."

Sai dai mai fashin baki kan al'amuran Afirka da ya kware a kan kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO Emmanuel Bensah ya shaida wa DW cewa, a wasu lokutan babu tabbacin kyamar mulkin mallaka na da nasaba da juyin mulkin da ake yi a Afirka na baya-bayan nan. A cewarsa rashin kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yada labarai masu karfi na taimakawa, yana mai cewa: "Abin da na fuskanta da kasashe rainon Ingila shi ne, suna da kungiyoyin farar hula masu karfi. Idan ka kalli kasashe kamar Ghana da Najeriya da Gambiya da Laberiya da Saliyo da sauran kasashe rainon Ingilan masu yawa, komai karancin kudin da suke fama da shi kamar a kasashen Laberiya da Saliyo za ka samu suna aiki sosai tare da hadin gwiwar kafafen yada labarai masu karfi da ke kokarin ganin mahukunta sun yi aikin da ya kamata.

Amma a kasashe rainon Faransa abin ba haka yake ba, tabbas akwai kafafen yada labarai. Misali a Senegal da ke zaman guda cikin kasashe rainon Faransa masu karfi, akwai kaafafen yada labarai da ke da tasiri amma kungiyoyin farar hula ba su da karfi sosai."

'Yan fafuiuka na nahiya Afirkar na kallon Faransa a matsayin mai yin zalunci

Masu zanga-zangar kyamar Faransa a Nijar
Masu zanga-zangar kyamar Faransa a NijarHoto: Stringer/Reuters

Ba kamar kasashe rainon Ingila da suka yi nisa a bangaren siyasa, tsarin dimukuradiyya irin na Kasashen Yamma bai samu kyakkyawan matsugun a kasashe rainon Faransa ba. Ibrahima Kane lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Senegal ya nunar da cewa: "Al'ummar kasashe rainon Faransa na tunanin masu mulki na dasawa da Faransa a koyaushe, akwai kwakwarar alaka tsakaninsu da gwamnatin Faransa. Gwamnatocin kan munzgunawa al'ummarsu, amma Faransa sai ta goyi bayansu. Wannan tunanin yana da tasirin gaske a tsakanin al'umma, suna kallonta a matsayin mai zalunci da kuma goyon bayan zalunci."

Zababbun shugabanni a kasashe rainon Faransan ba su yi wani abin azo a gani ga al'ummarsu ba

Masu zanga-zangar kyamar Faransa a Nijar
Masu zanga-zangar kyamar Faransa a NijarHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Sai dai dan jarida mai zaman kansa da ke bayar da rahotanni a kan Afirka ta Yamma Bram Posthumus  na da ra'ayi na dabam, kamar yadda yake cewa: "Akwai wani abu dabam da ke alakanta wadannan juyin mulkin da juna, kuma shi ne fannin da ba a mayar da hankali a kai. Juyin mulkin na radin kai ne, mafi yawa in ba duka ba sun yi ne saboda akwai banbamcin ra'ayi ta yiwu tsakanin shugaban kasar da ke kan mulki da kuma jagoran juyin mulkin. Misali a Nijar, an yi juyin mulki ne saboda hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na son sallamar wani babban sojan kasar daga aiki. dangane da batun Wagner kuwa, kamar sauran sojoji ko na Faransa ko Amurka da ma na Tarayyar Turai sun shiga ne saboda batun 'yan ta'adda.

Sai dai ba abin da suka yi, kasancewar ba a magance tushen matsalar ba wato batun matsin tattalin arziki musamman a tsakanin matasan yankunan." Da yake zantawa da DW, mai sharhi kan gwanatin Najeriya Ovigwe Eguegu ya nunar da cewa, zababbun shugabanni a kasashe rainon Faransan ba su yi wani abin azo a gani ga al'ummarsu ba. A cewarsa shi ne dalilin da ya sanya ake samun juyin mulki daga masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa, a ganinsa in har mutane ba su ga moriyar da za su ci daga mulkin dimukuradiyya ba to ba za a samun tallafin kirki daga gare su ba idan akka fada rikici.