1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi bayan mutuwar shugban kasar

Gazali Abdou Tasawa Ibrahim Tounkara/SB
June 11, 2020

A Burundi kwanaki kalilan bayan mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza, shugaban majalisar dokokin kasar zai jagoranci kasar a matsayin wucengadi kafin sabon shugaban kasar da aka zaba ya kama aiki.

https://p.dw.com/p/3de8B
Burundi Pierre Nkurunziza 2005
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

 

Kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ta Burundi ya tamnada, bayan mutuwar shugaban Pierre Nkurunziza, shugaban majalisar dokokin kasar Pascal Nyabenda ne zai shugabanci mulkin rikon kwarya kafin rantsar da sabon shugaban da aka zaba a watan Mayun da ya gabata wato Evariste Ndayishimiye wani na hannun damar Marigayi Nkurunziza. Babbar ayar tambaya dai a nan ita ce ko za a iya samun wani sauyi a karkashin sabon shugaban da ke shirin kama aiki. 'Yan adawa na kasar na cike da fata kan ganin sabon shugaban ya yi watsi da mummunar siyasar kuntatawa da kasar ta Burundi ta fuskanta a tsawon shekaru sama da 10 na mulkin jam'iyyar CNDD-FDD. Janvier Bigrimana wani lauya kana dan fafutika na kasar ta Burundi na daga cikin masu wannan fata.

Shugaba Nkurunzizza dai ya rasu ya bar kasar a cikin rikicin siyasa da matsalolin tattalin arziki. A dan haka a cewar Marie-Louise Baricako shugabar kungiyar mata da 'yan mata masu fafutikar zaman lafiya  akasar Burundi da ama  ke gudun hijira a yanzu haka a Ruwanda akwai manyan kalubalai a gaban mahukuntan kasar.

Burundi Evariste Ndayishimiye zum Sieger der Präsidentenwahl erklärt
Evariste Ndayishimiye shugaban Burundi mai jiran gadoHoto: Reurters/E. Ngendakumana

Sai dai wasu 'yan kasar ta Burundi na ganin wannan wata dama ce ga shugabannin sojin kasar na su maido da kimarsu da kuma mutuncinsu a idon 'yan kasar idan suka ba da hadin kai ga gina sabuwar tafiyar demokradiyyar kasar a yanzu, duk da yake cewa abin da kamar wuya a cewar Julia Grauvogel ta cibiyar binciken harakokin siyasa Afirka da ke a birnin Hamburg na Jamus.

A ranar 20 ga watan Agusta mai zuwa aka tsara za a rantsar da Evariste Ndayishimiye sabon shugaban kasar ta Burundi. Sai dai mutuwar ba zata da Shugaba Nkurunziza ya yi na iya saka mahukuntan kasar gaggauta rantsar da sabon shugaban kafin ranar da jadawalin farko ya tsaida.