1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brice Oligui Nguema ya kifar da Ali Bongo

Usman Shehu Usman AH
September 1, 2023

Batun juyin mulkin Gabon da Nijar sune suka fi daukar hankalin jaridun Jamus wadanda ke kallon cewar juyin mulki na kokarin zama ruwan dare a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4Vqp6
Sabon jagoran mulkin sojoji na Gabon Brice Oligui Nguema
Sabon jagoran mulkin sojoji na Gabon Brice Oligui NguemaHoto: AFP/Getty Images

Jaridar Neue Zürcher Zeitung wanda ta ce wani shaidani ya sauka a Afirka, bayan juyin mulkin soja a Gabon. Jaridar ta ce wannan karo sojoji sun sake kifar da gwamnati a mitstsiyar kasa mai mutane miliyan biyu da 300., amma kuma kasa da Allah ya horewa arzikin man fetur. Jaridar ta ce bayan sanar da sakamakon zabe sai sojoji suka ce haka ya isa wa mulkin iyalan Bongo wandanda ke mulkin kasar tun shekar tun 1967. Juyin mulkin ya zo yan mintuna bayan sanar da sakamakon zabe, sojojin sun karbe mulki a kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Gini, Chadi, Sudan da kuma yanzu kasar Gabon duk a kasashen Afirka cikin karamin lokaci. Jarida ta ce a yantu kama daga Yammacin Afirka.

Kungiyar EU ba ta goyi bayan kai hari ba a Nijar

Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Tchiani Abdourahamane tare da wasu na hannun damarsa
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Tchiani Abdourahamane tare da wasu na hannun damarsaHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta ce yanzu batun juyin mulki a Nijar sai dai a bi ta matsin lambar siyasa da diflomasiyya, amma babu batun amfani da karfi don mayar da gwamnatin Bazoum. Jaridar ta ce wannan ita ce shawarar da kungiyar Tarayyar Turai ta yanke taronta na karshe kan kawarta ta yankin Sahel da yanzu take neman yin asarar kawancenta. Amma dai sun daukin matakan kara takunkumai, yayin da ECOWAS kuma ke cewa a yi abin da ya fi takunkumi. JAridar ta ce a dai-dai lokacin da Kinistocin na Tarayyaar Turai ke fara ganawa a kasar Spain kan juyin mulkin Nijar, sai ga shi labarin wani juyin mulki a kasar Gabon, wanda daga can jami'an kasashen wanje na EU Josep Borrell ya ce ai kuwa labarin na Gabon in zama gaskiya to wani karin lamari ne da zai dagula zaman lafiya a yankin. Jaridar ta ce amma duk da cewa an yi juyin mulki a Gabon an yi ganawar ministocin na EU amma kuma sai suka zabi tattauna kasar bukatunsu yake wato Nijar. Inda aka kifar da gwamnatin shugaba Bazoum da ke biyan muradun Turai.

Ministar harkokin wajen Libiya da aka sauke daga mukaminta na cikin halin tsaka mai wuya

Nadschla al-Mangusch ministar harkokin wajjen Libiya da aka sauke daga mukaminta
Nadschla al-Mangusch ministar harkokin wajjen Libiya da aka sauke daga mukamintaHoto: Sotiris Dimitropoulos/ANE/Eurokinissi/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung, wace ita ma dai batun na juyin mulki ne, amma ita batun Farans ta fi karkata.Jaridar ta ce kasashen sun yanke siyasa da uwar gijiyarsu Faransa. Ta ce juyin mulkin Nijar, Paris na ganin to fa yanzu kuma karfin fada aji da ake da shi kan kasashen Afirka bisa al'ada a yanzu Faransa ta rasa wannan kwarjinin. Ko da shi ke ba Wanda ya son ya dorewar hakan zai kasance. Jaridar ta  ci gaba da cewa jakadan Faransa a Yamai yanzu haka dai kusan a cikin ofishinsa yake kwana, inda ake kareshi daga doguwar katangar Gini ofishin jakadancin, inda jami'an Jandarma ke sintiri a gefen katangar ba dare ba rana. Jaridar ta ce ko da shi ke gidan jakadan na Faransa yana tsallaken ofishin nasa ne, amma watakila kwana cikin ofishin ya fi tsaron lafiyarsa. Die Tageszeitung ta ce ganawar ministar harkokin wajen Libiya da Israi'la, ya jawo bore a kasar da ma kiran yin murabus. Bayan ganawar Nadschla al-Mangusch ministar harkokin wajen ta Libiya da takwaranta na Isra'ila hakan ya tada hankalin 'yan kasar Wanda ya sa shugaban gwamnatin Libiya tilasta mata barin aiki.