1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Maleriya a Afirka da shari'ar "Hotel Rwanda"

Suleiman Babayo MNA
September 24, 2021

Cutar Maleriya nan ci gaba da bijirewa magani a Afirka, mahawara a Namibiya kan yarjejeniyar sulhu da Jamus an kwace milyoyin kudin a Faransa da Switzerland daga mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea.

https://p.dw.com/p/40p8A
Ärzte ohne Grenzen | Krise in Zentralmali
Hoto: Mohamed Dayfour/MSF

Za mu fara da jaridar Bild wadda ta ce masu bincike sun gano yadda cutar zazzabin cizon sauro na Maleriya ke nuna tirjiya ga magani a nahiyar Afirka, inda magani ya daina aiki.  Masu bincike a kasar Yuganda da ke gabashin Afirka suka gano cewa galibin magunguna da aka kirkira domin yaki da cutar sun daina aiki, bayan gwajin da suka yi kan marasa lafiya 240. A shekara ta 2019 suka fara gano cewa kashi 20 cikin 100 na magungunan ba sa aiki. Kimanin mutane 400,000 ke mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a duk shekara kuma kashi 90 cikin 100 na adadin a kasashen Afirka suke, sannan fiye da mutane milyan 200 suke kamuwa da cutar duk shekara.

 Paul Rusesabagina lokacin zaman shari'arsa a kotu
Paul Rusesabagina lokacin zaman shari'arsa a kotuHoto: Muhizi Olivier/AP/picture-alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi mai taken "gwarzon da ya ceci mutane" lokacin kisan kare dangin Ruwanda da ya janyo aka yi fim mai suna "Hotel Rwanda" Paul Rusesabagina an same shi da laifin ta'addanci. Jaridar ta ce a cikin wata shari'a mai cike da rudani a birnin Kigali na kasar Ruwanda aka samu Paul Rusesabagina da laifin. An zarge shi da hannu wajen taimaka wa wata kungiya mai adawa da gwamnatin Ruwanda da kasar ta ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda. Shi dai Paul Rusesabagina ya yi suna sakamakon fim na "Hotel Rwanda" da ya ba da labarin yadda a matsayin manajan hotel ya ceci rayuwar daruruwan mutane daga kisan kare dangin Ruwanda na shekarar 1994, lokacin da wannan otel ya zama sansanin 'yan gudun hijira da ke samun kwarya-kwaryar kariya daga dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Zanga-zangar adawa da yarjejeniyar kisa kare dangi tsakanin Namibiya da Jamus
Zanga-zangar adawa da yarjejeniyar kisa kare dangi tsakanin Namibiya da JamusHoto: Sakeus Iikela/DW

Ana ta sharhin mai taken majalisar dokokin Namibiya ta koma mahawara kan batun rattaba hannu kan yarjejeniyar sasantawa da Jamus, jaridar die Tageszeitung ta ce yarjejeniyar tana cike da cece-kuce a kasar kan zargin kisan kare dangin da Jamus ta yi a Namibiya a farkon karnin da ya gabata. Inda masu adawa da yarjejeniyar suka yi zanga-zanga. Wasu 'yan kabilun Herero da Nama da abin ya shafa sun yi watsi da wannan tattaunawa tsakanin gwamnatin Namibiya da ta Jamus, inda suka koka da cewar an yi watsi da su a kan batun da ya shafesu kai tsaye.

Mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue
Mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang MangueHoto: Michele Spatari/AFP/Getty Images

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi kan milyoyin kudin da aka kwace a Faransa da Switzerland daga mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea. Jaridar ta ce kimanin kudin Euro milyan 150 da kadarori na Teodorin Obiang mataimakin shugaban kasar aka kwace bisa umurnin kotu a Faransa. Dan shekaru 53 da haihuwa ana zarginsa da halasta kudin haram a kasar da mahaifinsa ya shafe fiye da shekaru 40 kan madafun iko. Tun shekara ta 2011 kasar Amirka ta dauki matakin kan mataimakin shugaban kasar ta Equatorial Guinea wajen kwace kadarorin da ya mallaka a kasar da suka kai fiye da dalar Amirka milyan 30. Yayin da Amirka ta kwashe shekaru tana neman kulla yarjejeniyar yadda kudin zai koma ta hanyar da za a yi amfani da kudin wajen inganta rayuwar 'yan kasar.