1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan da Kwango a Jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
June 30, 2023

Yawan mace-mace a rikicin yankin Tigray na Habasha da yakin da ake fama da shi a Sudan da kuma hare-haren 'yan tawaye a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/4THy8
Habasha | Mekelle | Tigray | Rikici
Rikicin yankin Tigray na Habasha, ya halaka mutane da damaHoto: Million Hailessilasie/DW

Jaridan Berliner Zeitung cikin sharhinta mai taken "Adadin mace-mace mafi yawa tun bayan kisan kiyashin Ruwanda". Ta ce yake-yake sun yi sanadin mutuwar mutane dubu 238, galibi a  kasashen Habasha da Ukraine a bara. Wannan ya fito daga kididdiga kan zaman lafiya a duniya, wanda cibiyar IEP da ke nazarin tattalin arziki da zaman lafiya ta fitar. Jaridar ta ce tashin hankali da ya fi sanadin salwantar rayuka a shekarar da ta gabata, shi ne na yankin Tigray da ke kasar Habasha. Alkaluma sun nunar da cewa fiye da mutane dubu 100 ne aka kashe a fadace-fadacen da suka wakana a 2022. Sai dai abin takaicin ma a cewar jaridar shi ne yadda yawan mace-macen ya ninka sau biyu, idan aka lissafa wadanda cututtuka da yunwa suka yi sanadin mutuwarsu sakamakon arangama tsakanin sojojin Habasha da Iritiriya da 'yan tawayen TPLF.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango |  Rikici | M23 | Gudun Hijira
Mutane da dama na cikin tasku sakamakon rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Guerchom Ndebo/AFP/Getty Images

Ita kuwa die tageszeitung ta tabo rikicin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ne, wanda ta danganta da "Babbar barazanar tsaro." Jaridar ta ce ana samun karin dakaru masu shiga tsakani a wannan yaki, lamarin da ke kara haddasa rudani. Duk da cewa  kasashen Afirka sun tsara taro a Angola domin fayyace komai, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Ta ce shugabannin kasashen Afirka da dama da wakilan kungiyoyin AU da EAC ta gabashin Afirka da SADC ta kudancin Afirk sun bayar da gudunmawa wajen sasanta rigingimun da ke faruwa a gabashin Kwango, amma duk da haka tashin hankalin 'yan bindiga na karuwa baya ga adadin 'yan gudun hijira da ya ninka. Amma al'ummar yankunan da abin ya shafa, na kara nuna rashin gamsuwa da matakan wanzar da zaman lafiya da ake dauka. Ta ce ana hada kai da gwamnatin Kwango a duk lokacin da aka tsara wani sabon shirin wanzar da zaman lafiya a gabashin kasar, amma lamarin na rikicewa idan aka fara maganar aiwatarwa da shi. Ga misali, Kinshasa na son sojojin kasashen waje su taka rawa wajen yakar kungiyar tawaye ta M23, amma nauyin da aka dora musu shi ne tabbatar da tsaro a yankin.

Sudan | Rikici | Gwamnati | Sojoji | RSF
Har yanzu ana ci gaba da gwabza kazamin fada a SudanHoto: AFP via Getty Images

Da take tsokaci kan halin da ake ciki a Sudan jaridar Süddeutsche Zeitung ta danganta shi da "tsohon rikici da ya sanya jagororin yaki biyu kara karfi", inda ta ce shugaban kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan da babban hafsan mayakan sa-kai Mohammed Hamdan Daglo da ake wa lakabi da Hametti sun samo karfin fada a ji ne daga rikicin Darfur da ya salwantar da rayukan daruruwan 'yan tawaye da fararen hula shekaru 20 din da suka gabata. Jaridar ta ce duk da cewa rikicin na Darfur ba shi ne kadai aka fuskanta a Sudan ba, amma daya ne daga cikin mafi zalunci da ya gudana tsakanin manyan janar-janar na Larabawa da ke ruruta wutar daga Khartoum da kuma kabilun yankin da suke ganin cewar an mayar da su saniyar ware. Sai dai bayan faduwar mulkin Omar Hassan al-Bashir sakamakon tayar da kayar baya da al'ummar kasar suka yi a watan Afrilun 2019, al Burhan ya zama shugaban mulkin soja yayin da Hametti ya zama mataimakinsa. Jaridar ta ce wadannan janar-janar biyu, sune suka yi karan tsaye ga shirin mika mulki ga farfar hula kafin a samu tsamin danganta tsakaninsu.