1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa za ta harba taruraron dan Adam

Abdul-raheem Hassan
May 29, 2023

Japan na shirin ko ta kwana kan barazanar harba tauraron da Adam da Koriya ta Arewa ta sanar a makonni masu zuwa, sai dai Tokyo na ganin watakila makami mai linzami ne Pyongyang ke shirin cillawa.

https://p.dw.com/p/4RvZW
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un da 'yarsaHoto: KCNA via REUTERS

Pyongyang ta sanar da jami'an tsaron gabar tekun Japan cewa za ta kaddamar da makami mai linzami tsakanin ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni, kuma mai yuwa ya fada cikin kusa da tekun gabashin China da kuma gabashin tsibirin Luzon na kasar Philippines.

Ma'aikatar tsaron kasar Japan ta bayar da umarni ga rundunar sojin sama da ta kakkabo duk wani makami mai linzami da aka tabbatar yana barazana a yankin kasar.