1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Sumamen 'yan sandan a Kolon da Berlin

January 1, 2024

'Yan sandan Jamus sun sanar da cafke karin mutum 3 da ake zargi da shirin kitsa ta'addancin kai hari majami'ar nan mai tarihi wato Dome Cathedral da ke birnin Kolon.

https://p.dw.com/p/4al9q
Hoto: Christoph Hardt/Panama Pictures/picture alliance

'Yan sandan Jamus sun sanar da cafke karin mutum 3 da ake zargi da shirin kitsa ta'addancin kai hari majami'ar nan mai tarihi wato Dome Cathedral da ke birnin Kolon, a daidai lokacin da jami'an 'yan sandan ke ci gaba da sumamen masu son tada-zaune-tsaye a birnin Berlin.

An dai jibge jami'an 'yansanda  kimanin 1,000 a harabar  Majami'ar ta Kolon gabanin bukukuwan kirsimeti har zuwa bikin shiga sabuwar shekara ta 2024.

'Yan sanda a birnin Berlin kimanin 4,500 sun kwana cikin shirin tunkarar duk wata barazana da ka iya biyo bayan bikin shiga sabuwar shekara a birnin, da rahotanni suke ce an cafke mutane da dama da suka tayar da tarzoma a yayin bikin da wanda mutane da dama suka samu raunuka.