1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar MPLA na shirin lashe zaben Angola

Binta Aliyu Zurmi
August 26, 2022

A ci gaba da jiran cikakken sakamakon zaben shugaban kasar Angola da aka gudanar, dukkanin alamu na nuni da cewa jam'iyyar MPLA ta Shugaba Joao Lourenco da ke shugabancin kasar shekaru 47 na shirin lashe zaben.

https://p.dw.com/p/4G637
Angola | Präsident Joao Lourenco MPLA
Hoto: Stringer/REUTERS

Daga cikin kaso 97 cikin dari na sakamakon da aka kidanya, rahotanni na nuni da cewa Shugaba Joao Lourenco ya sami kaso 51 cikin dari a cewar hukumar zaben kasar.

Ita kuma a nata bangaren jam'iyyar adawa ta UNITA ta sami kaso 44 cikin dari na kuri'un da aka kai ga kirgawa. yayin da kananan jam'iyyu da ke rufa musu baya ke da sauran kason.

An sami karancin wadanda suka kada kuri'unsu a wannan zaben. Inda hukumar zabe mai zaman kanta tace kaso 45 na al'ummar kasar ne suka yi rajista zaben tun da farko, matakin da ke nuni da koma baya idan aka kwatanta da zaben da ya gabata.

Jam'iyyun MPLA mai mulki da UNITA dai, sun kwashe tsawon shekaru suna hamayya da juna tun gabanin samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka da kasar ta Angola ta yi.