1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar BJP a Indiya na son jan hankalin Musulmi a Kashmir

Suleiman Babayo MAB
April 18, 2024

Yayin da zabe ke gudana a Indiya a Afrilun 2024, jam'iyya mai mulki ta BJP na neman kwace yankuna daga hannun 'yan adawa ciki har da yankin Kashmir. Sai dai tana samun matsala wajen shawo kan Musulmi da ke kada kuri'a.

https://p.dw.com/p/4eviA
Firaminista Modi ya gudanar da tarurruka uku a Kashmir a cikin 'yan watannin baya
Firaminista Modi ya gudanar da tarurruka uku a Kashmir a cikin 'yan watannin bayaHoto: Sipa USA/picture alliance

Yakin neman zaben 2023 a yankin Kashmir ya zama na farko tun bayan watsi da kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai na lardin da gwamnatin kasar ta yi a shekara ta 2019. Ranar Asabar mai zuwa 19 ga watan Afrilu ne ake fara zaben 'yan majalisar dokokin kasar har zuwa farkon watan Yuni. Jam'iyyar Bharatiya Janata Party ta BJP mai ra'ayin kishin kasa ta Hindu ta Firaminista Narendra Modi na fatar samun nasara a wannan yanki na galibi Musulmai. 

BJP ta jaddada soke doka mai lamba 370

Musulmin yankin Kashmir na daukar zaben 2024 a matsayi makami a fannin siyasa
Musulmin yankin Kashmir na daukar zaben 2024 a matsayi makami a fannin siyasaHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Akwai masu zargin rusa ayar doka mai lamba 370 da ta bai wa yankin na Jammu da Kashmir sauya mazauna, yankin domin haka ya kawo karshen kwarya-kwaryar 'yanci da yin dokoki kan mallaka filaye, abin da gwamnatin kasar ta musanta. Robin Jeffrey, masanin siyasar Indiya kana marubuci da ke birnin Canberra na kasar Ostareliya, ya ce zaben kasar ta Indiya na wannan karon ya doraga ne kan abu guda: shi ne firaministan kasar: Ya ce: " Ina tsammani Mr Modi idan ba jam'iyyarsa take kan gaba ba, da za a yi zabe mai daukar hankali. Amma tun da yana kan gaba da jam'iyyarsa, kuma 'yan kasar Indiya suna ba shi goyon baya, ya zama shi ne abin da ake tattaunawa kuma masu zabe sun amince da haka."

Shi dai yankin Kashmir ya kasance wajen da ake samun sabani tsakanin Indiya da Pakistan inda duk bangarorin suke ikirarin mallakar daukacin yankin na Kashmir, amma kowace kasa na da wani bangaren na yankin na Kashmir da ke karkashin ikonta. A shekarun 1990, an samu tsageru dauke da makamai da suka kalubalanci Indiya a yankin da ke karkashin ikon kasar kuma har zuwa yanzu akwai kungiyoyin tsageru da suke aiki a yankin. A wata dabara ta siyasa har yanzu jam'iyyar BJP mai mulkin Indiya ba ta tantance ko dan takara guda ba daga cikin kujeru uku na yankin domin nuna cewa ba ta da karfin da take bukata a yankin na galibi Musulmai.

Babu wani kakkwaran bayani kan 'yan takarar BJP

Yankin Kashmir na fama da rikicin kan iyaka tsakanin Indiya da Pakistan
Yankin Kashmir na fama da rikicin kan iyaka tsakanin Indiya da PakistanHoto: Indranil Mukherjee/AFP

Jam'iyya mai mulki ta BJP karkashin Firaminista Narendra Modi na neman kara karfi ne kawai saboda irin karbuwa da ta samu a kasar, kamar yadda Sanjay Kumar na wata cibiyar kula da ci-gaba a kasar ke cewa duk da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa. Ya ce: "Masu zabe da yawa za su ce suna jin radadin tashin farashin kaya, amma za su ce wannan gwamnatin na kokari a wasu fannoni. 'Yan Hindu suna nuna alfahari da yanayin da ake ciki, galibi 'yan kasa 'yan Hindu ne, akwai alfaharin kishin kasa. Zama dan Indiya ya zama abin alfahari. Kimar Indiya ya habaka a duniya. Muna da shugaba mai karfin fada aji da ya daukaka sunan Indiya a duniya. Ina tsammani wannan ke zama abin da mutane suka daukan mataki a kai."

Har ta masu adawa da jam'iyyar BJP mai mulkin Indiya sun samu rarrabuwa duk da amince da dunkulewa wuri guda inda suka gaza samun dan takara guda da zai kalubalanci kuri'un da jam'iyya mai mulki za ta samu a yankin na Kashmir.