1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC na fama da dabaibayi a Najeriya

June 7, 2022

A Najeriya, yayin da jam'iyyar APC mai mulki ke gab da taron fidda gwani da zai ja ragamarta a babban zabe, ‘ya‘yanta na dada fadawa rikicin neman samun zakara mai sa'a.

https://p.dw.com/p/4CN1i
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar ta APC sun hadiye tabarya kuma sun kai ya zuwa kwana a tsaye. A cikin neman samu na magaji na shugaban kasar dake a zabe na badi. Duk da cewar dai fadar gwamnatin kasar na ci gaba a karatun kurma, rikicin na dada nisa yana kuma neman barazanar kare auren zobe a cikin APC.

Tuni dai shugaban jam'iyyar na kasa Abdullahi Adamu ya yi gaban kansa wajen bayyana shugaban majalisar dattawa na kasar Sanata Ahmed Lawal a matsayin dan takara na sulhu cikin jam'iyyar. Matsayin kuma da ya bata ran da dama kama daga ragowar yan majalisar zartarwar jam'iyyar ya zuwa ga ragowa ta magoya baya na bangarori d ayawa a cikin jam'iyyar.

Mustapha Mai Haja dai na zaman daya a cikin jiga-jigai na magoya baya na Bola Tinubu daga Yobe, da kuma ya ce ko a jihar tasu ba su shirin karbar shugabanci na Lawal din.

" Ba za mu karbi Ahmed Lawal ba, saboda an yi maganar cancanta ne kuma mu mun san Ahmed saboda ni mutumin Nguru ne,  kuma yanzu haka muna kuka da shi saboda rashin adalcin da ya yi mana. Ba mu adawa da an kai abu Gashua, to amma in aka kai Gashua ya kamata a kai Nguru a kai Yusufari a kai Machina. Mu mun san Ahmed Lawal ba zai mana adalci ba.”

Lagos Taslim Balogun - Bola Tinubu
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Ko bayan magoya bayan dai, ambato Lawal din ya sake hargitsa lamura cikin APC in da kama Tinubun da ke ganin cin ta a fili ya zuwa gwamnonin arewacin kasar da ke neman mulkin da ya yi kudu suke fadin matakin ya saba ka'idar jam'iyyar da kila dokar zabe ta kasar.

Abubakar Atiku Bagudu dai na zaman gwamnan Kebbi kuma shugaba na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC

" Bai tsai  da kowa ba, kuma har wa yau da muka ganshi ba yi matsaya ya ce ga wani nan a je a zabe shi ba. Mu ba mun ce ba ma son kujerar ba; muna so. Kuma wadanda ke nema daga arewa  suna da hakki kuma suna da cancanta da iyawa, kuma su ma hakuri muke ba su, bam u da ma ikon tilasta musu su janye. Hakuri muke ba su. Wasu masu takarar ma a cikinmu suke. Amma dai ba wata hujja ta talasta wa wani. Ko shi shugaban kasar ba ya iya tilastawa.”

Shawara irin ta daukar daki ko kuma rikici ganga-ganga dai, ‘yan awoyin da ke tafe dai na da tasirin gaske bisa makoma ta masu tsintsiyar da ko bayan rikicin cikin gida ke kuma fuskantar bore na waje. Wata kungiya ta matasa na arewacin kasar dai sun ce gwamnonin na shirin barar da damar APC a cikin zaben na badi sakamakon sayar da 'yancin na arewa da ke bukatar mulkin idanu a rufe.