1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Tawagar IAEA ta shiga tashar Zaporizhzhia

Abdoulaye Mamane Amadou
September 1, 2022

Makwanni bayan Rasha da Ukraine na zargin juna da kai farmaki a tashar makamashin Nukiliya ta Zaporizhzhia da ke Ukraine, tawagar hukumar IAEA ta fara aikin bincike a tashar

https://p.dw.com/p/4GJya
IAEO-Expertenmission besucht Kernkraftwerk Saporischschja
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Jami'an hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Majalaisar Dinkin Duiniya IAEA sun isa a babbar tashar makamashi ta Zaporizhzhia da ke Ukraine, a cigaba da binciken tashar mai tattare da hadari da tawagar ke shirin gudanarwa.

Kafar yada labaran Rasha ta Ria-Novosti ta wallafa wani faifan bidiyon da ke nuna tawagar a cikin motoci masu dauke da tambarin Majalisar Dinkin Duniya sun kusta a tashar a wannan Alhamis.

Kana kwararrun na bincike ne karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, duk da yake dakarun Rasha sun karbe riko da tashar mafi girma a nahiyar Turai tun bayan da suka fara mamayar Ukraine.